Babbar magana: Daya daga cikin makusantan mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence ya kamu da cutar Coronavirus
Daya daga cikin ma'aikata a ofishin mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence ya kamu da cutar nan mai kisa ta Corona, mai magana da yawun mataimakin ne ya bayyana haka jiya Juma'a da yamma
Duk da dai cewa ofishin na Pence bai bayyana ainahin sunan mutumin ko kuma mukamin da yake rike da shi ba, amma dai sanarwar ta bayyana cewa shine mutum na farko da ya kamu da cutar a fadar shugaban kasar, kuma hakan ya zo ne a lokacin da ake cikin damuwa dangane da lafiyar 'yan siyasa na birnin Washington, manyan ma'aikatan gwamnati da kuma wadanda suke yi musu aiki.

Asali: Facebook
Katie Miller, sakatariyar Mike Pence, ta ce:
"Yau da yamman nan mun samu labarin cewa daya daga cikin ma'aikatan ofishin mataimakin shugaban kasa ya kamu da cutar Corona. Sai dai daga shugaban kasa Donald Trump da mataimakinsa Mike Pence babu wanda ya hadu da wannan mutumi. Yanzu dai ana bincike akan mutanen da ya hadu da su."
Donald Trump ya zabi Pence domin ya jagoranci masu bincike akan Coronavirus na fadar shugaban kasar, wacce ake gabatar da rahoto a kullum.
An tabbatar da babu cutar dai a jikin shugaba Donald Trump bayan gwajin da aka gabatar a jikinsa, bayan ya gana da daya daga cikin manya a kasar Brazil a birnin Florida.
Da yawa daga cikin mutanen da suka hadu da dan kasar Brazil din wanda aka samu cutar a jikinsu an tabbatar da cewa suna gabatar da ayyukansu daga gida ne.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng