Yadda muke sayar da 'yan Najeriya a matsayin bayi a kasar Libya

Yadda muke sayar da 'yan Najeriya a matsayin bayi a kasar Libya

Wani mutumi dan jihar Kano da ya kware wajen safarar mutane musamman mata daga Najeriya zuwa kasar Libya domin suyi karuwanci, ya shiga hannun jami'an hukumar 'yan sanda

Vanguard ta ruwaito cewa wata mata mai shekaru 28 ita ma ta sha dakyar bayan 'yan sandan sun ceto ta daga hannun mutanen a lokacin da suka kama biyu daga cikin su a jihar Kano.

An gano cewa mutanen suna da mataimaka da yawa a ko ina na fadin kasar nan, inda suke daukar mata da nufin sama musu aiki mai kyau da kasar ta Libya.

Yadda muke sayar da 'yan Najeriya a matsayin bayi a kasar Libya

Yadda muke sayar da 'yan Najeriya a matsayin bayi a kasar Libya
Source: Facebook

Haka kuma an ruwaito cewa wadannan matan ba a bukatar su biya ko sisi wajen kai su kasar ta Libya, inda zasu hadu a jihar Kano, daga nan za a saka su a mota a shiga dasu kasar Nijar, daga Nijar za a shiga dasu kasar ta Libya da mota.

Wata majiyar ta bayyana cewa wadannan mutane suna da hadin guiwar wata kungiya a kasar Nijar, wadanda bayan sun karbe su Nijar za su sayar da su a matsayin bayi da za a dinga amfani dasu ana kwanciya da su na tsawon shekara biyu domin su biya kudin da aka kashe musu na zuwa kasar ta Libya.

Rundunar 'yan sandan da ta kama wadannan mutane wacce mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Abba Kyari ya jagoranta a ranar 20 ga watan Fabriaru, sun samu labarin mutanen, inda suka kama direban motar mai suna Abdullahi Umaru, wanda yake dauko matan daga Abuja zuwa Kano.

Abinda Umaru ya bayyana ya taimakawa jami'an wajen kamo shugaban wadannan mutanen mai suna Abubakar Suleiman, a jihar Kano, inda ita kuma Nofisat Mustapha, wacce suka dauko bayan sun yi mata karyar za su kai ta Libya su nema mata aiki ta samu ta kubuta a lokacin da suka kai ta jihar ta Kano.

A bayanin da yayi, Abubakar Suleiman ya ce; "Na fara safarar mutane shekarar da ta gabata, wani mutumi ne dan kasar Nijar mai suna Almusuru ya koya mini wannan sana'ar, amma yanzu shi ya koma kasar shi.

"Na tura masa sama da mutane 100 yanzu kuma a kowanne mutum daya ina samun naira dubu goma. Ban san daga inda mutanen suke zuwa ba, Almusuru shine yake magana da su a ko ina suke a fadin Najeriya, ni aikina kawai shine na kai su kasar Nijar Almusuru shi kuma zai biyani.

"Ban ma sani ba ko suna zuwa kasar Libya din a raye ko a mace ne ni ban sani ba. Na san babban laifi ne, amma ina yi ne saboda ina bukatar kudi," ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel