Coronavirus: Yadda aka hana shiga kotu sai an tantance lafiya (Hotuna)

Coronavirus: Yadda aka hana shiga kotu sai an tantance lafiya (Hotuna)

- Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bada umarnin cewa duk wanda ya ki amincewa a duba zafin jikinsa yayin tantancewa don shiga, da ya koma gida

- A wata sanarwa da aka manna a kofar shiga kotun ranar Juma'a dukkan wadanda za su shiga kotun an bukacesu da su yi biyayya

- Daya daga cikin likitocin da suke gwajin ya ce ba za a bar duk wanda zafin jikinsa ya wuce misali ba shiga kotun sannan kuma zai amsa tambayoyi

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bada umarnin cewa duk wanda ya ki amincewa a duba zafin jikinsa yayin tantancewa don shiga, da ya koma gida, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

A wata sanarwa da aka manna a kofar shiga kotun ranar Juma'a, dukkan ma'aikata da kuma baki da suka hada da lauyoyi, wadanda ake kara ko masu kara da 'yan jaridu, duk an bukacesu da su yi biyayya.

Coronavirus: Yadda aka hana shiga kotu sai an tantance lafiya (Hotuna)
Coronavirus: Yadda aka hana shiga kotu sai an tantance lafiya (Hotuna)
Asali: Twitter

Coronavirus: Yadda aka hana shiga kotu sai an tantance lafiya (Hotuna)
Coronavirus: Yadda aka hana shiga kotu sai an tantance lafiya (Hotuna)
Asali: Twitter

"Duk wanda ya ki amincewa a duba shi, dole ne ya koma gida. Kiyayewa ya fi magani," takardar ta bayyana.

Daya daga cikin likitocin da suke gwajin, ya ce duk wanda zafin jikinsa ya wuce misali, ba za a barshi ya shiga ba kuma za a ware shi don amsa tambayoyi a kan lafiyarsa da kuma inda ya ziyarta.

Tuni aka kafa bututun samar da sinadarin kashe kwayoyin cuta a kofar kowanne dakin kotu.

DUBA WANNAN: Yadda takalma suka tona wa wasu 'yan fashi da makami asiri a Zaria

Coronavirus: Yadda aka hana shiga kotu sai an tantance lafiya (Hotuna)
Coronavirus: Yadda aka hana shiga kotu sai an tantance lafiya (Hotuna)
Asali: Twitter

Coronavirus: Yadda aka hana shiga kotu sai an tantance lafiya (Hotuna)
Coronavirus: Yadda aka hana shiga kotu sai an tantance lafiya (Hotuna)
Asali: Twitter

A wani labari na daban, A yayin da cutar Covid-19 ke ci gaba da kamari a duniya kuma ana ci gaba da samun masu cutar a Najeriya, har yanzu babu wajen gwajin cutar a yankuna hudu cikin shida na kasar nan.

An gano cewa babu kayan gwajin cutar a yankunan Kudu maso gabas, Arewa maso yamma, Arewa maso gabas da kuma Arewa ta tsakiya duk kuwa da cewa ana ci gaba da tsoron yaduuwar cutar a cikin miliyoyin jama’ar da ke jihohin 19 na yankunan.

A dukkan kasar Najeriya, dakuna gwaje-gwaje biyar ne suke da kayan aikin gwajin cutar kuma suna nan ne a yankunan Kudu maso yamma da Kudu-kudu. An gano cewa akwai manyan dakunan gwaje-gwaje na gwamnatin tarayya guda biyu a jihohin Legas da kuma Osun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel