Kotun daukaka kara ta rage tsayin wa'adin garkame dan gwagwarmaya, IG Wala

Kotun daukaka kara ta rage tsayin wa'adin garkame dan gwagwarmaya, IG Wala

A ranar Jama'a ne wata kotun daukaka kara ta tarayya da ke Abuja ta rage tsayin wa'adin hukuncin daure dan gwagwarmaya, IG Wala, daga shekara bakwai zuwa biyu.

Wata babbar kotun tarayya ce da ke Abuja a karkashin mai shari'a, Jastis Yusuf Halilu, ta yanke wa Ibrahim Wala, wanda aka fi sani da IG Wala, hukuncin daurin shekaru bakwai a ranar 15 ga watan Afrilu na shekarar 2019.

Kotun ta yanke masa hukuncin ne bayan samunsa da laifin zargin shugaban hukumar jin dadin alhazai da cin hanci tare da jagorantar yi masa zanga-zanga.

Jastis Halilu ya samu IG Wala da laifuka uku daga cikin hudu da suka sa babban sifeton rundunar 'yan sanda da ministan shari'a suka gurfanar da shi.

Kotun daukaka kara ta rage tsayin wa'adin garkame dan gwagwarmaya, IG Wala

IG Wala
Source: UGC

Laifukan da aka same shi da aikata wa sun hada da tunzura jama'a, tattara jama'a ba bisa ka'ida ba, da kuma bata wa mutum suna.

Sai dai, Jastis Halilu ya yi watsi da tuhuma ta hudu da ake yi wa IG Wala saboda rashin gabatar da hujja mai gamsarwa.

An fara gurfanar da dan gwagwarmayar ne bayan shugaban hukumar jin dadin alhazai na kasa (NAHCOM), Abdullahi Mukhtar, ya yi korafi.

DUBA WANNAN: Coronavirus: Shugaba Buhari ya halarci sallar Juma'a a masallaci tare da jama'a

A cikin korafin, Mukhtar, ya zargi IG Wala da yin amfani da shafinsa na dandalin sada zumunta (facebook) domin bata masa da zubar da mutuncinsa da na hukumar da yake jagoranta.

IG Wala ya yi zargin cewa Mukhtar ya kulla harkalla da ta kai shi ga samun biliyan N3 daga kudin maniyyata aikin hajji na shekarar 2017, amma kuma ya gaza gabatar da hujja a gaban kotu bayan an gurfanar da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel