Coronavirus: Za a fara koyar da dalibai karatu ta gidan rediyo da gidan talabijin a jihar Legas
- Gwamnatin jihar Legas ta bayyana kudurinta na fara koyar da dalibai darasi ta gidajen rediyo da talabijin
- Gwamnati ta dauki wannan mataki ne bayan dakatar da makarantu da tayi sanadiyyar bullar cutar Corona a Najeriya
- Wannan sabon tsari na koyarwa zai shafi iya daliban ajin karshe ne na sakandare, wadanda za su rubuta jarrabawar WAEC
Kwamishinar ilimi ta jihar Legas, Mrs. Folasade Adefisayo, ta bayyana cewa sun fara gabatar da shirye-shirye da za a dinga koyarwa da daliban sakandare da suke ajin karshe darasi ta gidan rediyo da gidan talabijin.
A wata hira da tayi da LTV a Legas yau Juma'a, kwamishinar ta ce malaman makaranta za su dauki sautin darasin da suke koyawa dalibai guda takwas za a sanya su a gidajen rediyi da gidajen talabijin da kuma yanar gizo.
Jerin darasin da za su koyar sun hada da English Language, Mathematics, Biology, Chemistry, Physics, Literature In English, Financial Accounting da kuma Economics.
Folashade wacce ta shawarci makarantu gwamnati dana kudi da su bi dokar da aka saka ta rufe makarantu, ta kara da cewa:
"Kun san a makarantun mu da akwai yara da dama, kuma yara babu wanda ya isa ya hanasu wasa da junansu.
"Saboda haka mun saka dokar ne domin mu kare yaran mu, mun yadda kowacce makaranta ta rufe koyar da karatu har zuwa lokacin da zamu sanar a bude."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng