Na gaji da rayuwar nan gwanda mutuwa ta zo ta dauke ni - Mike Tyson

Na gaji da rayuwar nan gwanda mutuwa ta zo ta dauke ni - Mike Tyson

Fitaccen dan dambe na duniya Mike Tyson ya bayyana cewa a shirye yake mutuwa ta zo ta dauke shi, saboda rayuwa a wannan lokacin tayi wahala sosai, ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi

Kwanakin baya anyi hira da Tyson tare da Sugar Ray Leonard, inda ya nuna damuwarsa akan rayuwarsa ta baya yace yafi jin dadin rayuwarshi a lokacin da yake wasan dambe, yanzu da ya daina duk rayuwarshi ta lalace.

Yanzu abubuwan da fitaccen dan damben yake fada zai sanya mutane da yawa da suke bibiyarsa su tausaya masa.

A lokacin da yake cin karen shi babu babbaka, Tyson ya zama dan damben da kowa yake tsoro a duniya, yanzu dai ya zama sai dai a dinga yin labarinsa akan shaharar da yayi a duniya.

Na gaji da rayuwar nan gwanda mutuwa ta zo ta dauke ni - Mike Tyson
Na gaji da rayuwar nan gwanda mutuwa ta zo ta dauke ni - Mike Tyson
Asali: Facebook

Wata magana da yayi a lokacin da yake hira da The Sportsman za ta sanya kowa ya damu, inda ya ce:

"A gani na, da kuma abinda na yadda dashi, yawan tunanin da nake yi akan rayuwa ya sanya ina kawo mutuwa kusa gareni.

Da aka tambayeshi shin ya shirya mutuwa, Mike Tyson ya ce: "Kwarai kuwa bani tsoron mutuwa. Ina ganin rayuwa tafi mutuwa wahala a wannan lokacin kuma a gareni, rayuwa sai mutum ya sha wahala sosai.

"Idan baka yi da gaske ba rayuwa sai ta yiwa mutum wahala. Rayuwa tamkar tafiya ce, babbar kalubale ce. Mutane suna da komai na rayuwa amma kuma duk da haka suna wahala.

"Mun dauki kan mu kamar wasu mutane daban, bayan kuma mu ba koman komai bane, an halicce mu daga yunbu. Shin muna ganin mu wata halittace ta daban, yin suna a duniya ba komai bane.

"Bana tunanin wani abu marar kyau zai faru dani, amma duk lokacin da wani abu marar kyau ya faru ina dangana kuma ina neman mafita. Nayi abubuwa marasa kyau a baya haka rayuwata take.

"Idan wani abu marar kyau ya faru, ina dagewa naga nayi wani abu da zai amfaneni.

Wadannan sune kadan daga cikin maganganun da Mike Tyson yayi, muna fatan dai hakan yana nufin lafiyarshi kalau.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng