Jama’a sun karar da ‘maganin’ Coronavirus a Abuja da jahar Legas

Jama’a sun karar da ‘maganin’ Coronavirus a Abuja da jahar Legas

Jim kadan bayan sanarwar da shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya fitar na cewa masana masu bincike a kasar Amurka sun gano cewa maganin cutar zazzabin cizon sauro watau Chloroquine yana magnin Coronaviru, sai yan Najeriya suka fi mai kora shafawa.

Jaridar TheCable ta ruwaito wannan batu na Trump ya sa yan Najeriya musamnan a babban birin tarayya Abuja da jahar Legas neman maganin Chlorquine, har ta kai ga ana neman shi a shagunan magani amma babu shi, saboda jama’a sun saye shi.

KU KARANTA: Annobar Corona: Jerin Jahohi 13 a Najeriya da suka rufe makarantu tare da hana taron jama’a

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa sun fara samun nasara wajen inganta maganin zazzabin cizon sauro na Chloroquine a domin magance mugunyar annobar Coronavirus, cuta mai toshe numfashi.

“Nan bada jimawa ba zamu samar da wannan magani, kuma wannan wani fanni ne da hukumar kula da abinci da magunguna na kasar Amurka, FDA, ta nuna bajinta, kuma tuni an amince da sahihancin maganin.” Inji shugaba Trump.

Sai dai shugaban hkumar FDA, Stephen Hahn ya bayyana cewa basu kai ga samun cikakken amincewa ba tukunna, amma suna iya baiwa duk likitan da ya nema domin baiwa mara lafiya wanda Coronavirus ta kama shi, ba tare da bata lokaci ba.

Da wannan ne Stephen yace akwai sauran aikin da ake bukata a yi a kan maganin kafin a shigar da shi kasuwanni.

Wani mai shagon magani a jahar Legas, Chris Health Pharmacy ya bayyana cewa ya rasa dalilin da ya ga jama’a na ta tururuwa zuwa shagon domin sayen maganin Chloroquine.

“Kwali 20 nake da shi, amma zuwa yammcin alhamis sun kare kaf, mutum daya kadai ya sayi kwali 15, har ma yace zai dawo gobe don ya kara sayen wasu.” Inji shi.

Ita ma wata mata da ta sayi kwalaben ruwan maganin guda 6 ta bayyana cewa: “Dama an ce mana yana maganin cutar, amma bamu tabbatar ba sai shugaban kasar Amurka ya tabbatar, don haka na sayan ma yarana don na san nan bada jimawa ba farashinsa zai tashi.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng