Coronavirus: FG ta garkame manyan filayen jiragen samanta 3

Coronavirus: FG ta garkame manyan filayen jiragen samanta 3

- Gwamnatin tarayya ta rufe manyan filayen sauka da tashin jiragen samanta guda uku don shawo kan yaduwar cutar coronavirus a Najeriya

- Musa Nuhu, darakta janar na hukumar sufurin jiragen sama ta Najeriya (NCAA) ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis

- Ya ce za a rufe manyan filayen jiragen saman ne har sai baba ta gani kuma hakan zai fara ne daga ranar Asabar, 21 ga watan Maris

Gwamnatin tarayya ta rufe manyan filayen sauka da tashin jiragen samanta guda uku don shawo kan yaduwar cutar coronavirus a Najeriya.

Musa Nuhu, darakta janar na hukumar sufurin jiragen sama ta Najeriya (NCAA), ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis, kamar yadda jaridar The Cable ta wallafa.

Filayen jiragen saman uku da ta umarta a rufe sun hada da: Filin sauka da tashin jiragen sama na Mallam Aminu Kano da ke jihar Kano, filin sauka da tasin jiragen sama na Akanu Ibiam da ke jihar Enugu da kuma filin sauka da tashin jiragen sama na Omagwa da ke Fatakwal.

Ya ce za a rufe manyan filayen jiragen saman ne har sai baba ta gani kuma hakan zai fara ne daga ranar Asabar, 21 ga watan Maris.

Coronavirus: FG ta garkame manyan filayen jiragen samanta 3
Coronavirus: FG ta garkame manyan filayen jiragen samanta 3
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Buhari ya karba bakuncin shugaban majalisar dattijai da gwamnan jihar Yobe (Hotuna)

Amma kuma, ya ce filayen sauka da tashin jiragen saman na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da na Murtala Muhammed da ke Legas za su kasance a bude, amma ba jirgin da zai tashi ko ya sauka daga kasashen da cutar tayi kamari.

Wannan ci gaban ya biyo baya ne sakamakon umarnin gwamnatin tarayya na rufe dukkan manyan makarantun gaba da sakandire da na sakandire a fadin kasar nan.

Hukumomi dai a Najeriya na ci gaba da daukar matakai tsaurara don gujewa yaduwar mungunyar cutar.

A halin yanzu dai akwai mutane 12 a Najeriya da suka kamu da muguwar cutar da ta kashe a kalla mutane 10,000 a fadin duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel