Tsananin murnar nada sabon Sarki a Kano: Rarara ya sha alwashin raba motoci, babura, kudade da kujerun Makkah

Tsananin murnar nada sabon Sarki a Kano: Rarara ya sha alwashin raba motoci, babura, kudade da kujerun Makkah

Saboda shaukin cire Sarkin Kano Muhammadu Sanusi da maye gurbin sa da Aminu Ado Bayero, fitaccen mawakin nan Dauda Kahutu Rarara ya saka gasa, inda zai raba kujerun Makkah, motoci, babura da kudade kyauta ga wadanda suka yi nasara

Rarara ya bayyana hakane a wani sakon bidiyo da ya fitar a shafin sa na YouTube. Ya ce ya saka gasar ne don nuna farin ciki game da nada Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano da gwamnatin jihar ta yi.

Ya ce a ka'idojin shiga gasar ana so duk wani mawakin Hausa da yake Najeriya ko wajen ta da yayi sabuwar waka ga sababbin Sarakunan Kano guda biyar, wato na Kano, Bichi, Karaye, Gaya da kuma Rano.

A ka'idojin ana so kada wakar ta wuce minti biyar, sannan ya kasance a cikin minti biyar din nan mawakin zai yi wa kowanne Sarki wakar sa, cikin salo da zai burge kowacce fada, da kuma su kan su Sarakunan.

Wata ka'idar kuma ita ce tilas ne duk mawakin da zai shiga gasar ya kasance ya na da rijista da hukumar tace fina-finai ta jihar Kano.

KU KARANTA: Bayan bacewar mijinta da dadewa, ta ganshi tare da karuwarshi dauke da tsohon ciki

Bugu da kari kuma mutane 50 kacal za a zaba a matsayin zakarun gasar.

A cewar sa, a ranar da za a fidda zakarun kowanne mawaki zai zo da wakar sa a rubuce kuma ya rera ta a gaban manyan bakin da za su halarci taron, cikin su har da Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Rarara ya bayyana cewa ya tanadi farfesoshin nazarin harshen Hausa da za su zama alkalan gasar.

Ga dai jerin sunayen kyaututtukan da zai bawa wadanda suka yi nasara a gasar:

Na Daya: Mota

Na Biyu: Mota

Na Uku: Kujerar Hajji

Na Hudu: Kujerar Hajji

Na Biyar: Kujerar Umara

Na Shida: Kujerar Umara

Na Bakwai: Keke Napep

Na Takwas: Keke Napep

Na Tara: Babur

Na Goma: Babur

Sauran mawaka 40 da suka rage kuma kowannesu za a ba shi kyautar Naira dubu dari (N100,000).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel