Coronavirus: Aisha Buhari ta garkame ofishinta

Coronavirus: Aisha Buhari ta garkame ofishinta

- Uwar gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari, ta rufe ofishinta na makonni biyu

- Ta kara da bayyana cewa diyarta da ta dawo daga Ingila ta killace kanta duk da bata bayyana da alamar cutar ba

- Ta ce ta dau wannan matakin ne don biyayya ga shawarar ministan lafiya da kuma kwamitin karta-kwana na fadar shugaban kasa

Uwar gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari, ta rufe ofishinta na makonni biyu bayan wasu daga ciki hadimanta sun dawo daga tafiyar da suka yi zuwa Ingila.

Ta kara da bayyana cewa diyarta da ta dawo daga Ingila ta killace kanta, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, wacce ta wallafa wannan ci gaban a shafin na twitter, ta ce ta dau wannan matakin ne don biyayya ga shawarar ministan Lafiya da kuma kwamitin karta-kwana na fadar shugaban kasa a kan cutar Covid-19.

Ta rubuta: “Barkanmu da rana ‘yan Najeriya. Da farkon ranar yau Alhamis ne diyata ta dawo daga Ingila kuma kasar na daga cikin kasashen da aka lissafo a inda cutar Covid-19 tafi Kamari. Saboda shawara daga mai girma ministan lafiya, kwamitin karta-kwana na fadar shugaban kasa a kan cutar Covid-19 da kuma NCDC, ta killace kanta ba don ta bayyana da wata alamar cutar ba.”

Coronavirus: Aisha Buhari ta garkame ofishinta

Coronavirus: Aisha Buhari ta garkame ofishinta
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Ganduje ya kalubalanci hukuncin kotu a kan binciken Sanusi II

Ta kara da cewa, “Ina kira ga dukkan iyaye a kan su gane cewa , gujewa kamuwa da cutar yafi samun maganinta muhimmanci.”

“Hakazalika, na rufe ofishina na makonni biyu a take kuma hadimai za su iya aiki daga gida, don akwai wasu daga cikin ma’aikatan da suka dawo daga Ingila. Ina jinjinawa gwamnonin jihohin Arewa maso yamma tare da jihohin Neja da Kwara, ta yadda suka dau matakan hana yaduwar cutar a taron da suka yi a ranar Laraba a Kaduna.” Ta kara da cewa.

“Ina shawartarmu da mu ci gaba da bin shawarar ma’aikatar lafiya ta kasa da NCDC wacce ke kara kwarin guiwa wajen nisantar juna, wanke hannuwa da tsafta mai tsanani. Mu dau matakan kariya a kan iyalanmu da kuma jama’a baki daya. Akwai tabbacin zamu shawo kan matsalar annobar nan,” In ji ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel