Dan kasar Italiya da ya fara kawo cutar Corona Najeriya ya warke - Gwamnati

Dan kasar Italiya da ya fara kawo cutar Corona Najeriya ya warke - Gwamnati

Kwamishinan lafiya a jihar Legas, Farfesa Akin Abayomi, ya bayyana cewa sakamakon gwaji ya nuna cewa baturen nan dan kasar Italiya da ya fara shigo da kwayar da cutar Corona cikin Najeriya, ba ya dauke da kwayar cutar yanzu.

Ya bayyana hakan ne yayin wani taro da manema labarai a Legas, kamar yadda jaridar The Punch ta rawaito.

A cewar kwamishinan, za a sake gudanar da gwajin tantancewa na karshe a kan baturen tare da bayyana cewa za a sallame shi da zarar sakamakon gwajin ya sake nuna cewa ba ya dauke da kwayar da cutar.

An fara samun bullar kwayar cutar Coronavirus a ranar 27 ga watan Fabrairu, 2020, bayan baturen dan kasar Italiya da ke aiki a kamfanin simintin na Lafarge ya shigo da ita.

Kazalika, an tabbatar da sake samun kwayar cutar Cronavirus a jikin mutane hudu a jihar Legas a yau, Alhamis.

Kwamishinan lafiya a jihar, Farfesa Akin Abayomi, ne ya sanar da hakan yayin ganawarsa da manema labarai.

Dan kasar Italiya da ya fara kawo cutar Corona Najeriya ya warke - Gwamnati
Dan kasar Italiya da ya fara kawo kwayar cutar Corona Najeriya ya warke - Gwamnati
Source: Twitter

Abayomi ya bayyana cewa an samu mutane hudun ne daga cikin mutane 19 da aka yi wa gwajin kwayar cutar a ranar Laraba.

Ya kara da cewa an kebe mutanen hudu da aka samu da cutar a asibitin cututtuka masu yaduwa da ke Yaba, Legas.

Ya ce daga cikin sabbin mutanen da aka samu dauke da cutar akwa wata mata da ta kamu da kwayar da cutar daga wurin mata da ta zo daga kasar Ingila kwana biyu da suka wuce.

DUBA WANNAN: Muhimman abu uku da ya kamata ka gaggauta yi a halin yanzu - Shehu Sani ga Buhari

A cewarsa, akwai kuma wata mata da ta dawo Najeriya daga kasar Faransa ranar 14 ga watan Maris a jirgin kasar Turkiyya, TK1830.

Na uku daga cikin sabbin masu dauke da kwayar cutar, wani likita ne dan Najeriya da bai fita zuwa ko ina ba, amma aka same shi dauke da kwayar cutar.

Abayomi ya ce na hudun ma namiji dan Najeriya da aka gwada bayan ya dawo daga birnin Frankfurt, kasar Jamus, ranar 13 ga watan Maris.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel