Coronavirus: Kungiyar Ansaruddeen ta dakatar da Sallar Juma'a a masallatanta da ke fadin Najeriya

Coronavirus: Kungiyar Ansaruddeen ta dakatar da Sallar Juma'a a masallatanta da ke fadin Najeriya

Rahotanni sun kawo cewa kungiyar addinin Musulunci ta Ansarud deen a Najeriya ta dakatar da Sallar Juma'a da manyan taruka a masallatanta da ke fadin kasar sakamakon cutar coronavirus.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ranar Alhamis, 19 ga watan Maris, ta bayyana cewwa ta dauki wannan mataki ne cike da nauyin zuciya da kuma duba halin da ake ciki na dakatar da Salar Jum'a da kuma duk wani taro da ya wuce na mutum 50, shafin BBC Hausa ta ruwaito.

Ta ce dakatarwar za ta fara aiki ne ba tare da bata lokaci ba har sai abin da hali ya yi.

Kungiyar Ansaruddeen ta dakatar da Sallar Juma'a a masallatanta da ke fadin Najeriya
Kungiyar Ansaruddeen ta dakatar da Sallar Juma'a a masallatanta da ke fadin Najeriya
Asali: Twitter

A cewar sanarwar, matakin ya zama wajibi ne don hana yaduwar annobar coronavirus kamar yadda Kungiyar Malamai ta Duniya ta riga ta bayar da Fatawa a kai.

Har ila yau ta ce kungiyar za ta bi umarni da shawarwarin da gwamnati ta bayar amma za a sanar da jama'a duk wani ci gaba da ake samu game da matakin.

''Mun san cewa jama'a da dama ba lallai su ji dadin wannan labari ba, amma ya kamata su san cewa saboda ceton al'umma aka yi hakan.

''Don haka muna shawartar mutane da su ci gaba da yin sallolinsu a gidajensu su dinga bin matakan tsafta da sauran ayyukan ibadah,'' kamar yadda sanarwar ta kara.

Tun bayan da aka samu karin mutum biyar masu dauke da cutar a Najeriya ake ta daukar matakai daban-daban da suka hada da rufe makarantu a wasu jihohin.

A baya mun ji cewa Gwamnatin jahar Legas ta sanar da dakatar da gudanar da sallolin Juma’a da taron bauta na Kiristoci a wani mataki na kokarin yaki da yaduwar mugunyar annobar Coronavirus.

Daily Trust ta ruwaito kwamishinan harkokin cikin gida na gwamnatin, Anofiu Elegushi ne ya bayyana haka a ranar Laraba inda yace gwamnatin ta hana duk taro da ya haura mutane 50 a duk fadin jahar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel