Kisan sifetan 'yan sanda: Jama'ar Imasai sun fara gudun hijira

Kisan sifetan 'yan sanda: Jama'ar Imasai sun fara gudun hijira

Bayan kwanaki uku da harbe sifetan ‘yan sanda a Imasai da ke karamar hukumar Yewa ta Arewa a jihar Ogun, mazauna yankin suna ta barin gidajensu don gudun hijira sakamakon tsoron kama su da suke.

An samu mugun hargitsi ne a ranar Asabar a garin, sakamakon fada tsakanin jami’an tsaron iyakar kasa da wasu mazauna yankin wanda ya jawo kisan sifetan ‘yan sandan.

Amma kuma ‘yan sandan sun ce an kama mutane takwas da ke da hannu a wannan kisan, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Amma kuma a madadin mazauna yankin, shugaban yankin wanda ake kira da Atunluse na Imasai, Chief John Odu, da kuma wani mataimaki na musamman ga tsohon gwamna Ibikunle Amosun, Raheem Ajayi, sunce a halin yanzu garin ya zama abin tsoro.

Odu yayi ikirarin cewa an kashe daya daga cikin mazauna garin, kuma an birne shi yayin da sauran mazaunan yankin suka fara gudun hijira.

Odu ya yi ikirarin cewa, “Yan sandan sun shigo garinmu ne inda suka fara barna da sunan suna neman shinkafar da aka shigo da ita daga kasashen ketare.”

Kisan sifetan 'yan sanda: Jama'ar Imasai sun fara gudun hijira
Kisan sifetan 'yan sanda: Jama'ar Imasai sun fara gudun hijira
Asali: UGC

KU KARANTA: Sha'awar juna ce ta kama mu muka yi lalata - Wanda yayi garkuwa da matar aure

Shugaban ya zargi cewa jami’an tsaron sun tarwatsa bikin birne wani da ake yi a garin a ranar Asabar.

“Sun je har fadar sarkin garin Imasai din inda suka tarwatsata. Sun bincike gidan shi kakaf. Sun kashe mutum daya amma mun birne shi. Har yanzu dai mutane na cikin daji don ba zasu iya fitowa gari ba.” yace.

A yayin bayyana yadda lamarin ya faru, Ajayi wanda dan asalin garin ne ya kwatanta bayanin gwamnan jihar da na son bangare daya.

Tsohon mataimakin gwamnan na musamman ya ce, “Babu wanda ke goyon bayan kashe jami’an tsaro, hakazalika rayukan jama’armu tana da amfani. A don haka kuwa dole ne a mutunta kowacce rai. Gwamnatin jihar Ogun bata ambaci mutumin da aka kash ba, mutum daya da ke asibiti da kuma fadar Oba da aka wulakanta.

“A takaice dai yanzu haka kowa tsoron garin nan yake saboda fadan da aka yi da jami’an tsaro."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng