Gwamnatin Buhari ta kara ma manyan ma’aikata 1,583 girman mukamai

Gwamnatin Buhari ta kara ma manyan ma’aikata 1,583 girman mukamai

Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta amince da karin girma ga wasu manyan ma’aikatan gwamnati guda 1,583 a karkashin tsarin girma na matakin darakta na shekarar 2019.

Daily Trust ta ruwaito an bayyana hakan ne cikin wata sanarwa dake dauke da sa hannun shugaban hukumar ma’aikatan gwamnati, Dakta Tukur Bello Ingawa, inda take nuni da karin girma ga ma’aikatan mataki na 14 zuwa mataki na 15, yan mataki na 15 zuwa mataki na 16, sai yan mataki na 16 zuwa 17.

KU KARANTA: Jerin muhimmai matakai 13 da Buhari ya dauka tun bayan shigowar Corona Najeriya

A shekarar 2019 ne hukumar ta gudanar da jarabawar karin girma ga kwararrun ma’aikatan gwamnati da kuma jami’an kula da sha’anin mulki dake ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya, domin tsallakar dasu zuwa mataki na gaba.

Kaakakin hukumar, Felicia Eniola ta bayyana cewa sanar da sunayen wadanda karin girman ya shafa ya nuna muhimmancin da gwamnati ta sanya ga cigaban walwalar ma’aikata tare da tabbatar da ingancin tsarin aikin gwamnati.

A wani labarin kuma, Ministar kudi da tattalin arziki, Zainab Shamsuna Ahmed, ta bayyana hakan ne yayinda take hira da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan taron majalisar zantarwa da shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta ranar Laraba.

Ta ce gwamnatin tarayya za ta cigaba da biyan ma'aikata albashi kuma ba zata sallami ma'aikata ba amma ba za'a sake daukan sabbin ma'aikata ba.

Ta ce“Kan batun daukan aiki, an rigaya da bada umurnin dakatad da daukan aiki. Abinda ma'aikatun keyi dama na maye gurbin wadanda sukayi ritaya an dakatar.Idan abubuwa suka gyaru, zama'aikatuna cigaba. Amma yanzu albashin da zamu biya na da yawa.

“Shugaban kasa ya bada umurnin cewa a cigaba da biyan albashi da fanshi. Saboda haka bamu tunanin wani rage yawan ma“aikata.” Inji ta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel