Jerin muhimmai matakai 13 da Buhari ya dauka tun bayan shigowar Corona Najeriya

Jerin muhimmai matakai 13 da Buhari ya dauka tun bayan shigowar Corona Najeriya

Tun a watan Disambar shekarar 2019 ne aka fara samun bullar annobar cutar mao toshe numfashi ta Coronavirus a kasar China, inda daga nan ta watsu zuwa kasashe 151, daga ciki har da Najeriya.

Ita dai wannan cuta a yanzu haka ta kama sama da mutane 200,000 a duniya, tare da kashe akalla mutum 1000, kuma babban tashin hankalin shi ne har yanzu babu tabbacin takamaimen maganinta.

KU KARANTA: Gwamnatin Legas ta hana sallar Juma’a na tsawon makonni 4 saboda Corona

Bullar wannan cuta ta haifar da matsaloli da dama ga kasashen duniya, musamman ta bangaren tattalin arziki, inda ta sabbaba karyewar farashin gangan danyen mai a kasuwar duniya.

A nan gida Najeriya ma an samu bullar cutar a jikin mutane 8, don haka gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta dauki wasu muhimman matakai guda 13 domin kare yaduwar cutar ga jama’a da dama, daga cikinsu akwai;

- Hana baki yan kasashen waje shigowa Najeriya daga kasashe 13

- Dakatar da daukan aiki

- Hana jami’an gwamnati fita kasashen waje

- Rage farashin man fetir sakamakon karyewar farashin danyen mai

- Dakatar da bayar da bizan shigowa Najeriya

- Karfafa hukumar kare yaduwar cututtuka,NCDC

- Daktar da dukkanin wasannnin motsa jiki

- Dage gasar wasanni na kasa da za’a yi a jahar Edo

- Rage adadin kasafin kudin shekarar 2020 da kashi 20

- Rage hasashen farashin mai daga dala 57 zuwa dala 30

- Rage aikin hakar danyen mai daga cikin ruwa

- Rage kudin da gwamnati ke hasashen samu daga hukumar kwastam

- Rage kudin da ake hasashen samu daga sayar da kadarorin gwamnati

A hannu guda, kwamitin shugaban kasa dake yaki da yaduwar cutar Coronavirus ta kafa wata karamar kwamiti wanda za ta tattauna da shuwagabannin addinai daga bangarorin addinin Musulunci da kuma Kiristanci don duba yiwuwar kulle wuraren ibadu.

Ministan watsa labaru, Lai Muhammad ne ya bayyana haka yayin da yake bayar da jawabi game da shirye shiryen kwamitin a gidan talabijin na NTA, inda yace ba kai tsaye gwamnati za ta rufe wuraren ibada ba, har sai ta samu goyon bayan shuwagabannin addinai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel