Daga karshe: Buhari ya yi magana a kan fashewa bututun man fetur na Abule-Ado

Daga karshe: Buhari ya yi magana a kan fashewa bututun man fetur na Abule-Ado

A ranar Laraba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya da a gujewa aukuwa ibtila’in da duk za a iya kare kai daga shi a kasar nan.

Shugaban kasar ya ce, ya kamata a dau dukkan matakan da suka dace wajen ganin irin wannan masifar bata kara aukuwa ba a kasar nan.

Yayi wannan batu ne a yayin da ya je duba inda bututun man fetur na Abule-Ado ya fashe a jihar Legas.

Shugaban kasar, wanda ya samu wakilcin ministar walwala da jin kan ‘yan kasa, Sadiya Umar Farooq, ya yi alkawarin cewa gwamnatin tarayya za ta tallafawa wadanda hatsarin ya ritsa dasu.

Ya jajantawa jama’ar da gwamnatin jihar Legas a kan aukuwar lamarin.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kwatanta lamarin da abun bakin ciki kuma ya yi alkawarin tallafawa jama’ar da ya ritsa dasu don sake sabuwar rayuwa.

Daga karshe: Buhari ya yi magana a kan fashewa bututun man fetur na Abule-Ado

Daga karshe: Buhari ya yi magana a kan fashewa bututun man fetur na Abule-Ado
Source: Facebook

DUBA WANNAN: A raba ni da matata kafin in halaka ta - Magidanci ya sanar da kotu

“Gwamnatin tarayya tana son tallafawa gwamnatin jihar wajen sake gina yankin da gobarar ta shafa tare da tabbatar da cewa an samar da isassun magunguna ga wadanda ke kwance a asibiti sakamakon hatsarin.” ta bayyana.

Ya kara da jajanta wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a gobarar tare da addu’ar samun rahama garesu, kmara yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Daga karshe: Buhari ya yi magana a kan fashewa bututun man fetur na Abule-Ado

Daga karshe: Buhari ya yi magana a kan fashewa bututun man fetur na Abule-Ado
Source: Facebook

”Wannan lamarin da ya faru abun bakin ciki ne. Gani ya kori ji, da bamu zo ba, ba zamu san yadda abun yake ba. Ina so inyi amfani da wannan damar wajen bayyana muku cewa muna tare da shugaban hukumar kula da lamurran gaggawa ta kasa, NEMA da sauran cibiyoyi masu alaka. Zamu hada guiwa dasu ne wajen kawo kayan abinci da na talllafi ga jama’ar da abun ya shafa.” Ta ce.

Mataimakin gwamnan jihar Legas, Dr. Obafemi Hamzat wanda ya zagaya wajen da ministar, ya mika godiyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya turo ministan da sauran wakilan gwamnatin tarayya don ganin barnar da gobarar ta yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel