Kocin Atletico Portada Alta ya mutu a sakamakon cutar Coronavirus

Kocin Atletico Portada Alta ya mutu a sakamakon cutar Coronavirus

Mun samu labarin cewa Francisco Garcia, wani Matashin Kocin Kungiyar Atletico Portada Alta da ke Garin Malaga ya mutu a sakamakon cutar Coronavirus.

Francisco Garcia mai shekaru 21 ya kasance ya na horas da kananan ‘yan wasan kwallon kafan kungiyar ta Atletico Portada Alta kafin rasuwarsa a makon jiya.

Garcia ya dade ya na fama da larurar da a karshe aka gano cewa cutar dajin jini watau Leukemia ce. An iya gano wannan ne a lokacin da ya ke kwance a asibiti.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Independent ta kasar waje, an kwantar da Francisco Garcia ne bayan an same shi alamomin coronavirus.

Alamun wannan cuta ta Coronavirus sun bayyana a jikin Marigayin ne a sakamakon ciwon jinin da ya ke fama da ita. A karshe dai ya ce ga garinku nan a asibiti.

KU KARANTA: Masu dauke da cutar Coronavirus a kasar Saudi sun kai 230

Kocin kungiyar kwallon kafan ya mutu ne a Ranar Lahadi. Kungiyar Atletico Portada Alta ta fitar da jawabi ta na mika sakon ta’aziyya ga ‘Yanuwan Marigayin.

Haka zalika kungiyar Malaga ta aika sakon ta’aziyyar ta ga ‘Yanuwa da Abokan wannan Matashi da ya rasa ransa. Kungiyar ta ce dola ayi maganin COVID-19.

Hakan ya na nufin Garcia shi ne Mutum mafi karancin shekarun da wannan cuta ta kashe a Sifen inda cutar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 600.

Daga lokacin da Coronavirus ta barke a karshen bara zuwa yanzu, an samu mutane kusan 15000 da su ka kamu da cutar a kasar ta Kudu maso Yammacin Turai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel