Coronavirus: Sadio Mane ya taimakawa kasar Sanagal da kyautar £41,000

Coronavirus: Sadio Mane ya taimakawa kasar Sanagal da kyautar £41,000

‘Dan wasa Sadio Mane na kasar Sanagal, ya bada kudi har £41,000 ga kasarsa a matsayin gudumuwa domin a yaki cutar nan ta Coronavirus da ta ke ratsa Duniya.

Jaridar BBC Hausa ta bayyana wannan abin kirki da ‘Dan wasan gaban na Firimiya ya yi. Sadio Mane ya bada wannan gudumuwa ne domin a hana cutar yawo a Sanagal.

Mane ya na cikin masu yunkurin kira na ganin cewa an dauki lamarin cutar da muhimmanci. ‘Dan wasan ya kan fadakar da masu bibiyarsa a shafukansa na zumunta.

Kwanakin baya Mane ya fito kafafen sada zumuntan na zamani ya na kira ga jama’a su rika wanke hannuwansu domin gujewa kamuwa da wannan cuta ta Coronavirus.

A kasarsa ta Sanagal, akwai mutane fiye da 20 da su ke dauke da wannan cuta. Hukumomi sun bayyana cewa akwai mutane biyu daga cikin masu jinya da su ka warke.

KU KARANTA: Mike Obi ya tashi daga kungiyarsa bayan bullowar Coronavirus

Coronavirus: Sadio Mane ya taimakawa kasar Sanagal da kyautar £41,000
'Dan wasa mai tashe Sadio Mane ya ba Sanagal tallafin £41,000
Asali: Getty Images

A dalilin wannan annoba ne gwamnatin kasar Sanagal ta hana sauka da tashin duk wani jirgin sama da ya fito ko zai tafi kasashen Turai ko kuma wasu Yankin Afrika.

Kawo yanzu dai annobar ta yi kamari a kasashe irinsu Sin, Italiya, Sifen, Iran, da sauransu. Rahotanni sun bayyana cewa ana jinyar cutar a kasashen Duniya kusan 120.

A kasashen Arewacin Afrika irinsu Aljeriya, Masar, Tunisiya, ba a bari jirgin da ya fito daga Sanagal ya sauka. Wannan duk ya na cikin hanyoyin rage yaduwar cutar.

Idan aka yi lissafin gudumuwar da Mane ya ba kwamitin yakar cutar Coronavirus, kudin sun haura Naira miliyan 17. Ba dai yau Mane ya fara irin wannan taimako ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel