Gwamnatin Najeriya na neman hadin kan shuwagabannin addinai don kulle Masallatai da Coci

Gwamnatin Najeriya na neman hadin kan shuwagabannin addinai don kulle Masallatai da Coci

Kwamitin shugaban kasa dake yaki da yaduwar cutar Coronavirus ta kafa wata karamar kwamiti wanda za ta tattauna da shuwagabannin addinai daga bangarorin addinin Musulunci da kuma Kiristanci don duba yiwuwar kulle wuraren ibadu.

Ministan watsa labaru, Lai Muhammad ne ya bayyana haka yayin da yake bayar da jawabi game da shirye shiryen kwamitin a gidan talabijin na NTA, inda yace ba kai tsaye gwamnati za ta rufe wuraren ibada ba, har sai ta samu goyon bayan shuwagabannin addinai.

KU KARANTA: Sanatoci sun nemi Buhari ya fito ya ma yan Najeriya jawabi game da Coronavirus

“Bayan zaman farko na kwamitin, daga shawarwarin da aka bayar akwai bukatar kara hadin gwiwa tsakanin gwamnatocin jahoji, kananan hukumomi da kuma ta tarayya, haka zalika da kungiyoyin addinai, abokan cigaba da gidauniyoyi masu taimakawa.

“Idan har Saudi Arabia za ta iya rufe masallatan ta, banga dalilin da ba zamu iya rufe namu ba, idan dai wannan ne zai rage yaduwar cutar a tsakanin jama’a, amma dai ba zamu dauki wannan mataki ba sai mun tattauna da masu ruwa da tsaki.” Inji shi.

A hannu guda kuma, hukumar NYSC ta musanta rade radin da ake yayatawa ne cewa wai akwai wani dan bautan kasa daya kamu da cutar Coronavirus, inda ta ce babu gaskiya a cikin rade raden.

A ranar Laraba ne NYSC ta sanar da garkame dukkanin sansanonin horas da matasa masu yi ma kasa hidima dake fadin Najeriya tare da sallamar matasan daga sansanin.

Hukumar NYSC ta bayyana haka ne bayan wani taron gaggawa na masu ruwa da tsaki da suka gudanar a ranar Laraba, inda suka ce sun yanke shawarar kulle sansanonin horon yan bautan kasar ne saboda gudun yaduwar cutar Coronavirus.

A wani labarin kuma, majalisar dattawan Najeriya ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito ya yi ma yan Najeriya bayani game da bullar annobar cutar Coronavirus, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito majalisar ta yanke wannan shawara ne bayan wata doguwar muhawara a zauren majalisar a ranar Laraba, inda ta nemi gwamnatin Najeriya ta dauki kwararn matakai domin kare yaduwar cutar a Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel