Coronavirus: Gwamnonin Arewa maso yamma sun bada umarnin rufe makarantu na kwanaki 30

Coronavirus: Gwamnonin Arewa maso yamma sun bada umarnin rufe makarantu na kwanaki 30

Gwamnonin yankin Arewa maso yamma sun sanar da cewa za a rufe dukkan makarantu da ke yankin na tsawon kwanaki 30 kamar yadda The Nation ta ruwaito.

A cikin sakon bayan taro da gwamnonin suka fitar ta bakin shugaban kungiyar gwamnonin yankin, Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina, sun ce ya zama dole a dauki matakin hakan domin kare yaduwar cutar da Coronavirus a yankin.

An samu samu bullar wata cuta da ake zargin coronavirus ne a jihar ta Katsina a karo na farko a ranar Laraba.

Coronavirus: Gwamnonin Arewa maso yamma sun bada umarnin rufe makarantu na kwanaki 30

Coronavirus: Gwamnonin Arewa maso yamma sun bada umarnin rufe makarantu na kwanaki 30
Source: UGC

DUBA WANNAN: Budurwa ta sa an damke mutumin da ya taba mata nono a motar haya

Gwamnonin sun yi taro ne a Kaduna tare da hukumomin tsaro domin yin bita kan tsare-tsaren samar da tsaro a yankin kafin rahoton bullar cutar ya fito a Kaduna a safiyar ranar Laraba.

Gwamna Masari ya ce za a rufe makarantun daga ranar Litinin 23 ga watan Maris.

Ya ce gwamnonin za su zauna da hukumomin shirya jarrabawa su tattauna da su kan lamarin.

Sun kuma shawarci al'umma su guji taron mutane idan ba da muhimmin dalili ba kana su cigaba da tsafta.

Kazalika a wurin taron, Masari ya kungiyar gwamnonin tare da hadin gwiwa da hukumomin tsaro za su sake yin bitan tsarin da suke amfani da shi na yaki da kallubalen tsaro da ke adabar yankin.

Wani sabon abinda gwamnonin suka amince da a kai shine kafa wata tawagar tsaro na hadin gwiwa tsakanin jihohi bakwai na Arewa maso yamma da jihar Niger.

Da ya ke magana a kan yiwuwar bullar ta Coronavirus a jihar Katsina, Masari ya ce mara lafiyar da ake zargin yana dauke da kwayar cutar ya killace kan sa kafin zuwa lokacin da sakamakon gwajin zai fito.

Sakataren dindindin na ma'aikatar Lafiya na jihar Katsina, Dakta Kabir Mustapha ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a ranar Laraba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel