Kamata yayi a dinga kai 'yan siyasa suna yin kwana daya ko biyu a gidan yari kafin a basu mulki - Sanata Suswam

Kamata yayi a dinga kai 'yan siyasa suna yin kwana daya ko biyu a gidan yari kafin a basu mulki - Sanata Suswam

A cewar tsohon gwamnan jihar Benue kuma Sanata mai wakiltar jihar Benue, Sanata Gabriel Suswam, kamata yayi 'yan siyasa su fara yin kwana daya ko biyu a gidan yari, hakan zai saka su yiwa mutane aiki

Sanatan wanda a yanzu hukumar yaki da cin hanci da rashawa take bincikarshi akan badakalar naira biliyan uku da ya cinye a lokacin da yake gwamna jihar Benue, ya bayyana hakane a lokacin da yake magana akan cunkoson gidan yari, wanda Sanata Uche Ekwunife, dake wakiltar Anambra ta tsakiya ya gabatar.

Da yake bayyana abinda ya gani a gidan yarin, Suswam, ya sanar da cewa zai fi a dinga kai 'yan siyasar Najeriya gidan yari na dan lokacin domin su ga yadda rayuwa take kafin a basu mulki.

Ya ce: "Zan bayar da goyon baya akan abinda na gani da idona a lokacin da nake gidan yari, ina ganin domin 'yan siyasa su yiwa mutane aiki da kyau a kasar nan, ya kamata a kai dukkanmu gidan yari domin muyi kwana daya ko biyu."

Cikin dariya shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya ce: "wadanda suka yi gwamna a baya ba, da kuma wadanda suka rike mukamin mataimakin gwamna." Ya ce kafin Suswam ya cigaba.

KU KARANTA: Jennifer Haller: Mace ta farko a duniya da aka fara gwada maganin Coronavirus a jikinta

"Na je ni can, an kai ni can da dare. Gari na wayewa kowa a cikin gidan yarin ya san da zuwana.

"Na zauna a can tun daga safe har dare, saboda akwai mutane da yawa a wajen.

"Zaku yi mamakin yadda suke shafe shekaru da yawa a wannan waje. Akwai wani matashi dana hadu dashi wanda yayi shekaru 10 akan wata matsala ta naira dubu goma kawai.

"Mutane da yawa na wajen saboda laifi kalilan da suka aikata, inda na tabbata 'yan sanda zasu iya gyarasu su aika su gida.

"Na sanya a zuciyata cewa a ranar da na bar wannan waje, a cikin wata daya na fitar da mutane kusan ashirin daga wannan waje. Ba wani abu bane mai wahala, kawai ka biya kudin ka tura su kotu."

Wannan magana dai ta cunkoson gidan yarin an gabatar da ita ne domin majalisar ta duba yiwuwar gyare-gyare a gidajen yarin na fadin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel