Jennifer Haller: Mace ta farko a duniya da aka fara gwada maganin Coronavirus a jikinta
Wata mata mai shekaru 43 a duniya ta zama mutum ta farko a duniya da aka yiwa allurar gwajin maganin cutar Coronavirus
Bayan fara gabatar da gwajin, Jennifer Haller ta zama ta farko da aka fara gabatar da gwajin a jikinta.
Gwajin wanda aka fara shi kwanan nan, Dr Lisa Jackson ta jagoranci gwajin, wacce take babbar ma'aikaciya a cibiyar lafiya ta Seattle dake birnin Washington, birnin da yafi ko ina yawan mutanen da suka kamu da cutar a kasar Amurka, inda mutane 42 suka mutu a cikin mutane 69 na kasar.

Asali: Facebook
Jennifer Haller ta yi magana akan wannan gwaji da aka gabatar a kanta, inda ta ce:
"Hankalin mu duka a tashe yake saboda wannan cutar, saboda haka nake ganin kamar wannan wata dame ce a wajena a fara gabatar da gwajin a kaina."
KU KARANTA: Na rasa gidana, katafaren shagona da manyan motoci na alfarma sanadiyyar gobar Legas - Jaruma Umeh
An zabi mutane wadanda za a gabatar da gwajin a kansu da suke tsakanin shekaru 18 zuwa 55, inda ba wai iya lafiyar maganin za a duba ta maganin ba, ana so a gano yadda mutum zai yi bayan gabatar da gwajin a jikinshi.
Nan da makonni shida, za a sake gabatar da gwajin akan mutane 45.
Wannan dai na zuwa ne bayan cutar ta Coronavirus wacce ta samo asali a kasar China ta girgiza ko ina na kasashen duniya.
Cutar wacce a yanzu ta shiga kusan dukanin kasashen duniya an kasa gano ainahin maganinta. Sai dai a wannan karon kasar ta Amurka ta gabatar da gwajin a karon farko.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng