Na rasa gidana, katafaren shagona da manyan motoci na alfarma sanadiyyar gobar Legas - Jaruma Umeh

Na rasa gidana, katafaren shagona da manyan motoci na alfarma sanadiyyar gobar Legas - Jaruma Umeh

- Fitacciyar jarumar Nollywood ta bayyana irin asarar da tayi sanadiyyar gobarar da ta faru a jihar Legas

- Jarumar ta ce abinda yafi ba ta mata rai shine yadda kafafen sadarwa da gwamnati suka ki bayyanawa duniya gaskiyar lamarin

- Amma ta ce ta godewa Allah da ta tsira da rayuwarta, kuma tana sa ran Allah zai kawo hanyar da za ta mayar da dukiyarta

Fitacciyar jarumar fina-finan kudancin Najeriya (Nollywood) Nkiru Umeh ta wallafa wani rubutu a shafinta na Instagram, inda take bayani akan asarar da ta tafka sanadiyyar gobarar da ta faru a jihar Legas ranar Lahadi.

Umeh ta wallafa wani dan takaitaccen bidiyo na shagonta da gidanta da gobarar ta kone, inda kuma tayi rubutu a kasa kamar haka.

"Katafaren shagona da gidana suna kallon makarantar mata ta Bethlehem kuma gobarar ta faru a daidai gaban makarantar. Komai ya kone. Amma na gode Allah dana tsira da raina.

"Har yanzu lamarin yana damuna, amma abinda yafi bata mini rai shine yadda kafafen sadarwa da gwamnati suke yiwa mutane karya akan lamarin. Zan yi bayanin wannan abu idan hankalina ya dawo jikina, domin a yanzu haka jikina duk rawa yake.

KU KARANTA: Mijin da ya ci amanar matarshi yaje yayi zina da wata a titi ya dauko cutar Coronavirus a jikinta

"Allah ya nuna mini cewa ni daban nake da kowa, ya nuna mini yadda yake sona, na rasa gidaje guda biyu, motoci biyu da kaya na kimanin naira miliyan goma. Katafaren shagona kayan dake ciki sun kai kimanin na naira miliyan 50. Kuma tabbas gidana da kowa ya sanshi musamman wadanda suka shiga sun san yadda yake da kyau.

"Ba komai, tunda har ina nan da raina, ina da mijina, 'ya'yana, masu aikina da kowa suna nan da ransu. Saboda haka cikin ikon Allah duka wadannan abubuwa Allah zai maye gurbinsu da wasu. Amma babu wanda ya isa ya dawowa da mutum rayuwa idan ya mutu. Saboda haka ina kara godiya ga Allah."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel