Zargin badakala: Kotu ta tsayar da ranar fara sauraron korafin tsohon sarki Sanusi II

Zargin badakala: Kotu ta tsayar da ranar fara sauraron korafin tsohon sarki Sanusi II

A yau Laraba ne wata babbar kotun tarayya da ke zama a jihar Kano ta saka ranar 23 ga watan Maris don ci gaba da sauraron karar da tubabben sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya mika a gabanta na bukatar ta dakatar da hukumar korafi da yaki da rashawa ta jihar a kan bincikarsa.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, Sanusi ya mika bukatar ne gaban kotun a kan ta dakatar da shugaban PCACC, Muhyi Rimingado, Antoni janar din jihar Kano da Gwamna Abdullahi Ganduje daga bincikarsa.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriyan ya ruwaito cewa, a ranar 6 ga watan Maris ne kotun ta dakatar da PCACC a kan bincikar Sanusi tare da bukatarta da ta tsaya har sai an ci gaba da sauraron shari'ar.

Wadanda ake karar sun hada da hukumar korafi da yaki da rashawa ta jihar Kano, Muhyi Rimingado, Antoni janar din jihar Kano da gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Amma kuma idan zamu tuna, hukumar sauraron koke da yaki da rashawa ta jihar Kano ta ce za ta ci gaba da bincike a kan tubabben sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II, bayan umarni daga kotu.

Zargin badakala: Kotu ta tsayar da ranar fara sauraron korafin tsohon sarki Sanusi II

Zargin badakala: Kotu ta tsayar da ranar fara sauraron korafin tsohon sarki Sanusi II
Source: Twitter

DUBA WANNAN: An bayyana shirin tsohon sarki Sanusi II na gaba bayan tube rawaninsa

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa wata babbar kotun tarayya da ke zama a Kano ta hana hukumar bincikar tubabben sarkin a kan zarginsa da ake da damfarar naira biliyan 2.2.

Shugaban hukumar, Barista Muhuyi Rimingado ya sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a jiya Talata, cewa ana ci gaba da bincike.

"Ko a ranar Litinin hukumar ta gayyaci wasu kamfanoni kuma duk sun zo. Amma kuma za a ci gaba da bincikar tubabben sarkin bayan umarni daga kotu," Rimingado yace.

Yace tube sarkin zai sa hukumar ta samu damar yin bincike ba tare da wani katsalandan ba ko wani shinge. "A halin yanzu muna da sararin bincike tunda babu sarkin a kusa," ya kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel