Sanatoci sun nemi Buhari ya fito ya ma yan Najeriya jawabi game da Coronavirus

Sanatoci sun nemi Buhari ya fito ya ma yan Najeriya jawabi game da Coronavirus

Majalisar dattawan Najeriya ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito ya yi ma yan Najeriya bayani game da bullar annobar cutar Coronavirus, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito majalisar ta yanke wannan shawara ne bayan wata doguwar muhawara a zauren majalisar a ranar Laraba, inda ta nemi gwamnatin Najeriya ta dauki kwararn matakai domin kare yaduwar cutar a Najeriya.

KU KARANTA: Nan bada jimawa ba za mu fara daukan sabbin Yansanda 10,000 – Minista

“Majalisa ta yi kira ga shugaban kasa ya fito ya yi ma yan Najeriya bayani game da wannan matsalar, manyan kasashen duniya sun yi haka, idan ya fito yayi jawabi ga yan Najeriya, sai an fi daukan maganan da muhimmanci.

“Ba wai mun ce babu abinda take yi bane, amma akwai bukatar gwamnati ta dauki kwararan matakai kamar su hana tafiye tafiye, hana wasu kasashe shigowa kasa, rufe iyakokin kasar, rage taruwar jama’a, tsaurara binciken masu shigowa kasa da kuma killacesu tsawon makonni biyu.

“Haka zalika akwai bukatar majalisar ta baiwa gwamnatin Najeriya dukkanin goyon bayan da take bukata don yaki da cutar, a bude cibiyoyin gwaje gwaje, a hana kamfanonin jiragen sama na kasashen waje tashi daga Najeriya, a kulle filayen sauka da tashin jiragen Najeriya banda Abuja da Legas.”Inji shi.

Sanata Danjuma Goje na jahar Gombe ne ya gabatar da wannan kuduri a gaban majalisar, inda yace akwai bukatar gwamnatin tarayya, gwamnatin jahohi da gwamnatocin kananan hukumomi su sanya idanu kamar yadda hukumomin kiwon lafiya suka tanada.

A cewar Goje: “Ina ganin jahohin Legas, Ogun da gwamnatin tarayya sun yi kokari wajen magance matsalar yaduwar cutar, amma hakan bai isa ba, saboda manyan kasashen duniya suna ta daukan matakan tsaro game da kare cutar COVID-19.”

A natawa jawabin, Sanata Oluremi Tinubu ta bayyana cewa: “Ya kamata mu lura da yadda muke mu’amala da mutane, saboda Allah Ya mana baiwa, ku tuna lokacin Ebola, amma ba zamu ce mun bar komai a hannun Ebola ba.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel