‘Dan kwallo John Mikel Obi da kungiyar Trabzonspor sun raba gari

‘Dan kwallo John Mikel Obi da kungiyar Trabzonspor sun raba gari

Mun samu labari daga Reuters a farkon makon nan cewa ‘Dan wasa John Obi Mikel ya tattara ya bar kungiyar kwallon kafa na Trabzonspor da ke kasar Turkiya.

‘Dan wasan tsakiyan ya nuna cewa hankalinsa bai kwanta ba game da yadda kungiyar ta Trabzonspor ta ke cigaba da buga wasanni a irin wannan lokaci.

Duk da dar-dar da aka shiga a dalilin barkewar cutar Coronavirus, har gobe ana cigaba da wasanni a kasar Turkiya, wannan ya tadawa ‘Dan wasan hankali.

Babbar kungiyar ta Super Lig ta tabbatar da cewa John Obi Mikel ya bar ta. Trabzonspor ta fitar da wannan jawabi ne a kan shafinta na yanar gizo a Ranar Talata.

Jawabin kungiyar ya nuna cewa Mikel Obi ‘Dan asalin kasar Najeriya wanda ya koma taka leda a kulob din a bara, ya tashi bayan an ci ma yarjejeniya a makon nan.

KU KARANTA: Gwaji ya nuna cewa Matuidi ya na dauke da Coronavirus

‘Dan kwallo John Mikel Obi da kungiyar Trabzonspor sun raba gari
Mikel Obi ya bar kungiyar Trabzonspor saboda gudun kamuwa da cuta
Asali: Getty Images

Duk da Mikel Obi ya na da ragowar kwantiragi da kungiyar har zuwa shekarar 2021, ‘Dan wasan tsakiyan ya bukaci datse wannan kwangila da ya rattaba hannu a bara.

Mikel mai shekara 32 a Duniya ya yi magana a shafinsa na Instagram tun Ranar Asabar, 14 ga Watan Maris, ya ce: “Akwai wata rayuwar ta dabam bayan kwallon kafa.”

“Ba na jin hankali na ya natsu, kuma ba na son buga kwallo a wannan yanayi. Ya kamata kowa ya koma cikin gidansa tare da Iyalinsa da Masoya a wannan lokaci.”

John Mikel Obi ya bada shawarar a daina buga duk wasu wasanni saboda wannan annoba. “A dakatar da wasannan kakar nan a lokacin da Duniya ta ke fama”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel