Mashawartan Buhari sun gargade shi game da afkawa halin tabarbarewar tattalin arziki

Mashawartan Buhari sun gargade shi game da afkawa halin tabarbarewar tattalin arziki

Kwamitin mashawartan shugaban kasa a kan tattalin arziki ta gargadi shugaban kasa Muhammadu Buhari game da yiwuwar Najeriya ta sake fadawa cikin mawuyacin halin tabarbarewar tattalin arziki.

Jaridar Punch ta ruwaito majalisar a karkashin jagorancin Farfesa Doyin Salami ta gana da shugaba Buhari ne a ranar Talata a fadar gwamnatin Najeriya, inda ta bayyana masa cewa matukar ba’a magance yaduwar cutar Coronavirus ba, tattalin arzikin Najeriya zai fada mawuyacin hali.

KU KARANTA: Annobar Lassa ta halaka mutane 8, babban Likita da wani hakimi a jahar Bauchi

A cewar kwamitin, babbar manuniya game da haka it ace karyewar farashin gangar danyen mai a kasuwar duniya da kuma koma baya da aka samu ga cigaban tattalin arziki, sa’annan nan gaba kadan masu zuba jari zasu dakata saboda basu da tabbacin yadda yanayin kasuwanci zai kasance.

Bugu da kari, kwamitin ta bayyana ma Buhari cewa gaba kadan wasu matsaloli zasu kara tasowa kamar su yawaitan danyen mai a kasuwar duniya, hauhawar matsalar rashin aikin yi, raguwa a asusun ajiyan kudaden gwamnayi da kuma janyewar gwamnatoci daga gudanar da kasuwanci.

Don haka majalisar ta nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rage adadin kasafin kudin bana domin a samu daman daidaita tattalin arzikin kasar, yin haka ne kadai zai kare afkawa cikin tabarbarewar tattalin arziki.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adeshina ne ya bayyana haka bayan tattaunawar da kwamitin ta yi da Buhari, inda yace ta nemi gwamnati ta mayar da hankali wajen kashe kudi a kiwon lafiya da manyan ayyukan more rayuwa.

Sai dai a nasa bangaren, shugaba Buhari ya jaddada ma yan Najeriya manufarsa na tabbatar da kasar ta fita daga cikin wannan kalubale lafiya, tare da kawar da duk wasu matsaloli da ka iya tasowa a dalilin karyewar farashin man.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel