Nazir Sarkin wakar San Kano ya ajiye sarautar da Sanusi ya bashi

Nazir Sarkin wakar San Kano ya ajiye sarautar da Sanusi ya bashi

A irin tataburzar dake faruwa a jihar Kano sanadiyyar tsige tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, har ya zuwa yanzu dai lamarin yaki lafawa

Yayin da wasu ke murna da samun dami a kala, wasu kuwa sun koma gefe ne takaici ya dame su, duka sanadiyyar tsige Sarkin da gwamnatin jihar Kano tayi a 'yan kwanakin da suka gabata.

Wata takarda da muka samu tana ta faman karakaina a shafukan sadarwa na zamani ta bayyana yadda Nazir Ahmad Sarkin Wakar San Kano ya ajiye mukaminsa da tsohon Sarki Sanusi ya bashi.

Nazir Sarkin wakar San Kano ya ajiye sarautar da Sanusi ya bashi

Nazir Sarkin wakar San Kano ya ajiye sarautar da Sanusi ya bashi
Source: Facebook

Takardar wacce aka rubuta ta a ranar 13 ga watan Maris dinnan tayi bayani kamar haka:

KU KARANTA: Mata Musulmai sune suka fi kowanne mata tsafta da tsarki a duniya - Bincike

"Bismillahir Rahamanir Rahim!

"Na rubuta wannan takarda domin na sanar da hukuncin dana yanke na yin murabus daga mukamina na 'Sarkin Wakar San Kano', wanda zai fara daga yau 13 ga watan Maris na shekarar 2020. Ina godiya matuka akan wannan mukami da aka bani ba wai iya ga masarautar Kano ba, ina godiya ga jihar baki daya.

"Haka kuma, ina godiya ga masarautar da irin damar da ta bani na yin aiki da ita tsawon shekara daya da wani abu, wannan wata dama ce dana samu da kuma zan cigaba da cin ribarta har karshen rayuwata.

"Ina fatan zaku yi na'am da wannan hukunci da godiya tawa.

"Na ku a koda yaushe,

"Alhaji Nazir Muhammad Ahmad."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel