Coronavirus: Blaise Matuidi ya kamu da COVID-19 inji Juventus

Coronavirus: Blaise Matuidi ya kamu da COVID-19 inji Juventus

Labarai sun zo mana daga Jaridar Bleacher Report cewa ‘Dan wasan kasar Faransa Blaise Matuidi ya kamu da cutar nan ta Coronavirus da ke yawo yanzu.

Kungiyar Juventus ta sanar da cewa Blaise Matuidi ya na dauke da kwayar cutar COVID-19. Blaise Matuidi shi ne ‘Dan wasa na biyu da cutar ta kama a cikin kungiyar.

A makon da ya gabata ne aka tabbatar da cewa ‘Dan wasan bayan Juventus, Daniele Rugani ya kamu da cutar. Rugani shi ne ‘Dan wasan da ya fara kamuwa a Seria A.

Bayan nan ne ‘Yan wasa da-dama har da irinsu Tauraro Cristiano Ronaldo su ka shiga boye kansu. Bayan an yi gwaji, an tabbatar da cewa Ronaldo bai dauke da cutar.

Sai a jiya Ranar Talata ne kungiyar Italiyar ta fito ta bayyana cewa wani ‘Dan kwallon na ta watau Blaise Matuidi ya kamu da cutar numfashin, amma ya na murmurewa.

KU KARANTA: Kocin Arsenal Arteta ya na cikin wadanda su ka kamu da Coronavirus

Coronavirus: Blaise Matuidi ya kamu da COVID-19 inji Juventus
'Yan wasa biyu sun kamu da Coronavirus a Juventus
Asali: Depositphotos

Kungiyar Juventus ta fitar da jawabi ne a daren Ranar Talatar nan. “An yi wa Blaise Matuidi gwajin asibiti, an kuma gano cewa akwai cutar COVID-19 a cikin jikinsa.”

Jawabin ya kara da cewa: “Tun daga Ranar 11 ga Watan Maris 2020, ‘Dan wasan ya kasance ya killace kansa da kansa. Za a cigaba da kula da shi a wannan marra.”

A karshen jawabin, kungiyar kwallon kafan ta bayyana cewa alamomin wannan cuta ba su bayyana a jikin ‘Dan wasan mai shekaru 32 ba, kuma ya na samun sauki.

Yanzu haka dai an dakatar da gasar Seria A a kasar ta Italiya. Ana sa ran cewa idan abubuwa sun yi sauki za a cigaba da wasannin kwallon kafan a farkon Watan Afrilu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel