Kisan kiyashin Auno: Majalisa ta bukaci ganin Buratai da gaggawa

Kisan kiyashin Auno: Majalisa ta bukaci ganin Buratai da gaggawa

- Majalisar wakilan Najeriya ta fara bincike a kan harin da aka kaiwa masu ababen hawa da mazauna kauyen Auno a ranar 9 ga watan Fabrairun 2020

- Kwamitin na bukatar shugaban rundunar sojin Najeriya, Tukur Buratai da yayi bayanin abinda ya kai ga harin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito

- A yayin martani, Buratai, wanda ya samu wakilcin shugaban horarwa da ayyuka na rundunar sojin, Manjo Janar E.O Udom, ya tabbatar da cewa wadannan bayanan da aka bukata za su samu

Majalisar wakilan Najeriya ta fara bincike a kan harin da aka kaiwa masu ababen hawa da mazauna kauyen Auno a ranar 9 ga watan Fabrairun 2020.

Kwamitin majalisar a kan rundunar sojin Najeriya, wanda Abdulrazak Namdaz dan jam'iyyar APC daga jihar Adamawa ke shugabanta, ya kira shugaban rundunar sojin Najeriya, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai.

Kwamitin na bukatarsa da yayi bayanin abinda ya kai ga harin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kisan kiyashin Auno: Majalisa ta bukaci ganin Buratai da gaggawa
Kisan kiyashin Auno: Majalisa ta bukaci ganin Buratai da gaggawa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Budurwa ta sa an damke mutumin da ya taba mata nono a motar haya

Namdaz ya jajanta rashin rayuka da kuna barnar da aka samu a yayin harin 'yan Boko Haram din. Ya ce kwamitinsa ya ziyarci Auno sannan sun samu saduwa da jama'ar da abun ya shafa, tare da taimaka musu. Sun kara da duba yawan barnar da aka samu.

Ya ce kwamitin na bukatar rundunar sojin da ta bayyana musu bayanai masu amfani ko kuma su bayyana tsarin da suke amfani dashi na yakar ta'addanci wanda har yasa komai ke kara ta'azzara.

A yayin martani, Buratai wanda ya samu wakilcin shugaban horarwa da ayyuka na rundunar sojin, Manjo Janar E.O Udom, ya tabbatar da cewa wadannan bayanan da aka bukata za su samu.

Idan zamu tuna, a ranar 9 ga watan Fabrairun 2020 ne mayakan Boko Haram suka kai hari ga jama'ar kauyen Auno inda suka tare masu ababen hawa da ke kan babban titin.

Tuni mayakan kuwa suka fara kisar mutanen ta hanyar yi musu yankan rago. Lamarin da ya jawo tsananin firgici da dimuwa ga mazauna yankin Arewa maso gabas din kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel