Mutuwar mahaifiya: Buhari ya jajanta ma gwamnan Kogi, Yahaya Bello

Mutuwar mahaifiya: Buhari ya jajanta ma gwamnan Kogi, Yahaya Bello

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya gwamnan jahar Kogi, Yahaya Bello alhinin rashin mahaifiyarsa, Hajiya Hauwa Bello wanda ta rasu a ranar Lahadi, 17 ga watan Maris a garin Okene.

A jawabinsa, kamar yadda Premium Times ta ruwaito, shugaba Buhari ya yi kira ga iyalan Hajiya Hauwa da su daina jimamin mahaifiyar tasu, saboda ta yi rayuwa mai kyau, don haka kamata yayi su yi murnar kyakkyawar baya da ta bari.

KU KARANTA: Annobar Lassa ta halaka mutane 8, babban Likita da wani hakimi a jahar Bauchi

Buhari ya bayyana haka ne yayin taron addu’an uku na mamaciyar da ya gudana a garin Okene a ranar Talata, inda ya ce gibin da marigayiya Hauwa ta bari ba zai yiwu a cika shi a nan kusa ba, don haka ya yi fatan Allah Ya baiwa iyalanta hakuri.

Shugaban wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari yace: “Za’a tuna marigayiya Hajiya Bello da irin gudunmuwa da goyon bayan da ta baiwa dan ta gwamnan jahar Kogi, musamman a shekaru hudu da suka gabata.

“Don haka nake kira ga gwamnan da sauran yaranta su tabbata sun sanya ta a cikin addu’o’insu a kowanne rana domin samun gafara da rahamar Allah Ubangiji” Inji shi.

Daga cikin wadanda suka raka Abba Kyari zuwa taron addu’ar akwai Ministan watsa labaru, Lai Muhammad, Ministan ayyuka na musamman, George Akume, karamar ministar Abuja, Ramatu Tijjani, hadimin shugaban kasa a kan harkar watsa labaru, Garba Shehu.

A nasa jawabin, Gwamna Bello ya bayyan godiyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa yadda ya nuna damuwarsa da rasuwar mahaifiyarsa, sa’annan ya bayyana dawainiyar da babarsa ta yi da shi bayan rasuwar babansa sun yana dan wata hudu.

Ya kara da cewa kokarin da yake yi na tabbatar da adalci a mulkinsa da kuma zaman lafiya a jahar Kogi ya biyo bayan goyon bayan da mahaifiyarsa take bashi tare da karfafa masa gwiwa da take yi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel