Kotu ta gargadi tsohon miji ya daina kai wa tsohuwar matarshi ziyarar dare

Kotu ta gargadi tsohon miji ya daina kai wa tsohuwar matarshi ziyarar dare

- Wata kotun shari'a da ke Magajin Gari a Kaduna ta umarci wani dan kasuwa mai suna Salisu Sani a kan ya daina zuwa gidan tsohuwar matar shi

- Alkalin mai suna Murtala Nasir ya kara da umartar Sani, wanda ya amsa laifin da ake tuhumarsa a kan ya gujewa zagin tsohuwar matar shi din

- Matar mai zama a Kinkinau ta bayyana cewa tsohon mijinta din ya je har gidansu inda ya dinga zaginta tare da yi mata mugun duka

Wata kotun shari'a da ke Magajin Gari a Kaduna ta umarci wani dan kasuwa mai suna Salisu Sani, a kan ya daina zuwa gidan tsohuwar matar shi mai suna Zainab Abdullahi, ballantana da dare.

Alkalin mai suna Murtala Nasir ya kara da umartar Sani , wanda ya amsa laifin da ake tuhumarsa a kan ya gujewa zagin tsohuwar matar shi din, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Ya ce dukkan su biyun su kiyay juna tare da fita lamurran juna.

An maka Sani a gaban kotun ne bayan tsohuwar matar shi tayi korafin cewa ya je gidansu ya zageta tare da yi mata mugun duka

Kotu ta gargadi tsohon miji ya daina kai wa tsohuwar matarshi ziyarar dare

Kotu ta gargadi tsohon miji ya daina kai wa tsohuwar matarshi ziyarar dare
Source: UGC

DUBA WANNAN: Kayattacen hoton tsohon Sarki Sanusi da iyalansa bayan saukarsa daga mulki

Mai gabatar da shari'a, Aliyu Ibrahim, ya sanar da kotun cewa mai koken wacce take zama a Kinkinau Kaduna ,ta kai karar tsohon mijinta ne a ofishin 'yan sanda na Magaji gari da ke Kaduna.

Ya ce wacce ta kai karar ta sanar da 'yan sandan cewa a ranar 13 ga watan Maris ne tsohon mijinta mai suna Sani Salisu ya isa har gidansu inda yayi mata mugun duka.

"Ya kira ta da karuwa a gaban jama'a sannan yana amfani da wayar tafi-da-gidanka wajen turomin sakonni da zasu iya zubar mata da mutunci. Wannan kuwa ya ci karo da sassa na 273, 239 da 272 na dokokin Penal code na jihar Kaduna na shekarar 2017," mai gabatar da kara ya sanar.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, a ranar 13 ga watan Maris din ne kotun ta bada belin Sani a kan kudi har N100,000 tare da gabatar da wani wanda zai tsaya masa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel