Mambobi 5 da aka dakatar a majalisar Kano sun mayar da martani

Mambobi 5 da aka dakatar a majalisar Kano sun mayar da martani

Mambobin majalisar dokokin jihar Kano guda biyar da aka dakatar a ranar Litinin, sun bayyana dakatarwar da aka yi musu a matsayin wasan yara da kuma yi wa doka 'karan tsaye'.

A ranar Litinin ne shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Abdulazeez Garba Gafasa, ya sanar da dakatar da mambobin majalisar bisa zarginsu da nuna rashin tarbiya da kuma karya dokokin majalisa.

Da yake magana da manema labarai da yammacin ranar Litinin, wakilin mambobin da aka dakatar, Mohammed Bello, daga mazabar Rimin Gado, ya ce dakatarwar da aka yi musu ta saba wa doka.

"Mu na gida mu na shirin fito wa majalisa kamar koda yaushe sai kawai samun labari muka yi kan cewa an dakatar mu na tsawon wata shida.

"Babu wata doka ta majalisa ko ta kasa da ta bawa majalisar ikon dakatar da mu ta wannan hanya.

Mambobi 5 da aka dakatar a majalisar Kano sun mayar da martani

Majalisar dokokin jihar Kano
Source: Facebook

"Dole kafin a dakatar da mamba daga majalisa, idan ya yi laifi, sai an tsamo laifin tare da tura shi gaban kwamitin da'a da ladabtarwa na majalisa domin su kira shi ya kare kansa.

"Idan kwamitin bai gamsu da hujjojin dan majalisar ba, sai ya mika rahotonsa gaban majalisa domin jin ra'ayin mambobi a kan matakin da ya kamata a dauka, kuma sai kaso biyu cikin uku na mambobin majalisar sun amince kafin a zartar da hukunci.

DUBA WANNAN: Babu gudu, babu ja da baya a niyyarmu ta fita daga jam'iyyar APC - Tsohon gwamna

"Duk basu bi wadannan ka'idoji ba, bayan haka sabawa doka ne a ce shugaban majalisa ya sanar da dakatar da mu.

"Har yanzu ba a bamu takardar dakatarwar ba, sai sun aiko da takardar sannan zamu san mataki na gaba da zamu dauka," a cewarsa.

Rahotanni sun bayyana ceewa mambobin biyar da aka dakatar sun hada da uku daga jam'iyyar APC da kuma biyu daga jam'iyyar hamayya, PDP.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel