Yanzu-yanzu: Buhari ya dakatar da bikin wasanni na Najeriya na 2020 saboda Coronavirus

Yanzu-yanzu: Buhari ya dakatar da bikin wasanni na Najeriya na 2020 saboda Coronavirus

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da dage bikin wasanni na kasa (NSF) da aka yi wa lakabi da Edo 2020 a matsayin wani mataki na kare yaduwar cutar Coronavirus a kasar.

Ministan Wasanni na Najeriya Sunday Dare ya sanar da cewa za a dage wasanni na kasar da aka shirya yi a Birnin Benin na jihar Edo.

'Yan wasa a dukkan jihohin kasar sun dade suna shirin zuwa Birnin Benin domin hallartar wannan wasannin kafin sanarwar ta fito a ranar Talata 17 ga watan Maris.

DUBA WANNAN: Kayattacen hoton tsohon Sarki Sanusi da iyalansa bayan saukarsa daga mulki

Ya ce, "Bayan ganawar da na yi da Shugaban kasa tare da karamin ministan Lafiya game da cutar COVID 19, Shugaban kasa ya amince da dage da bikin wasanni na kasa da za a gudanar a Edo zuwa wani lokaci a nan gaba.

"Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da dage wasanni na kasa Edo 2020 a matsayin matakin hana yaduwar cutar COVID 19.

"An dage wasannin kasa da za a gudanar a Edo."

Najeriya ta tabbtar da samun bullar cutar ta COVID-19 karo na uku a ranar Talata 17 ga watan Maris na 2020.

An tabbatar da kwayar cutar ne a jikin mace 'yar Najeriya da ta dawo kasar daga Birtaniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel