An bayyana shirin tsohon sarki Sanusi II na gaba bayan tube rawaninsa
- Sananne a kafar yada labarai, Dele Momodu a ranar Litinin ya kai wa tubabben sarkin Kano, Sanusi Lamido ziyara a Legas
- A yayin ziyarar da Momodu ta kai wa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya din, ya ce sam wannan hukuncin na gwamnatin jihar Kanodin bai bata wa basaraken rai ba
- Sananne a kafar yada labarai ya bayyana cewa, a halin yanzu Sanusi na kokarin ganin yadda zai amfani al'umma ne da gogewarsa
Sananne a kafar yada labarai, Dele Momodu a ranar Litinin ya kai wa tubabben sarkin Kano, Sanusi Lamido ziyara a Legas.
Sanusi, wanda ya samu 'yancinsa bayan wata babbar kotu a Abuja ta yanke hukuncin gaggawar sakinsa, a halin yanzu yana jihar Legas.
A yayin ziyarar da Momodu ta kai wa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya din, ya ce sam wannan hukuncin na gwamnatin jihar Kano bai bata wa basaraken rai ba.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Rusau: Jama'ar jihar Kaduna sun yi wa El-Rufai ihun 'Bama yi', 'Bama so' (Bidiyo)
Sananne a kafar yada labarai ya bayyana cewa, a halin yanzu Sanusi na kokarin ganin yadda zai amfani al'umma ne da gogewarsa.
Idan zamu tuna, Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a cikin sa'o'i 48 bayan tubewa tsohon sarkin Kano din rawani, ya bashi mukamai har biyu a jihar.
A shafinsa na twitter, Momodu ya rubuta: "Na dau lokaci mai inganci da amfani a tare da tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II da wannan yammacin. Yana cike da burin ci gaba kuma bai nuna damuwarsa ba a kan abinda ya faru.
"Ya zabi ci gaba da ayyukan da zasu amfani al'umma da gogewarsa hadi da iliminsa. Ina masa fatan alheri."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng