Babu gudu, babu ja da baya a niyyarmu ta fita daga jam'iyyar APC - Tsohon gwamna

Babu gudu, babu ja da baya a niyyarmu ta fita daga jam'iyyar APC - Tsohon gwamna

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Segun Oni, ya ce ba zai janye shawarar da ya yanke na fice wa daga APC ba saboda kaskancin da ya ce shi da magoya bayansa na fuskanta a cikin jam'iyyar.

Segun ya bayyana cewa ba a bashi wani girma a cikin APC a matsayinsa na tsohon mataimakin shugaba jam'iyyar na kasa da aka dakatar ba bisa ka'aida ba. Kazalika, ya bayyana cewa babu shakka tsohuwar jam'iyyarsa, PDP, zai koma.

A tattaunawarsa da jaridar Tribune ta wayar tarho ranar Litinin, Segun ya ce yanke shawarar fita daga jam'iyyar ne domin kare mutuncin magoya bayansa da ba a ganin kimarsu a cikin jam'iyyar APC, a saboda haka an hana su mukamai a cikin jam'iyyar.

"Ba don kaina nake son fice wa ba, zan bar APC ne saboda magoya bayana da suke son yin siyasa amma an hana su dama a cikin jam'iyyar. Ba a ganin kimarsu, ba a basu mukamai a cikin jam'iyyar APC.

Babu gudu, babu ja da baya a niyyarmu ta fita daga jam'iyyar APC - Tsohon gwamna

Segun Oni
Source: Twitter

"Haka ake tafiyar da jam'iyya? kawai sai a ware wasu 'yan jam'iyya a hana su mukamai saboda kawai su yaran Segun Oni ne.

DUBA WANNAN: Abinda yasa aka tsige tsohon sarki Sanusi II- Tanko Yakasai

"Haka kurum wasu mutane suka ce sun dakatar da ni daga jam'iyya. Har yanzu ba a kara waiwayen batun dakatarwar da aka yi min ba

"Dole mu yi yaki da rashin adalci da danniya da ake nuna wa wasu rukuni na 'yan jam'iyyar. Ta yaya wasu mutane da basu da mukamin komai a cikin jam'iyya zasu taru kawai su sanar da dakatar da shuaga a cikin jam'iyya?," a cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel