Coronavirus: Ghana ta kulle dukkan makarantu da jami'o'inta
A ranar Litinin, kasar Ghana ta kulle dukkan makarantu da jami'o'inta da duk wani taro domin takaita yaduwar cutar Coronavirus da ta addabi duniya wannan shekaran.
Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, ya sanar da hakan ne ga alummar kasar cewa za a kulle makarantun har ila ma shaa Allahu.
Bugu da kari, an dakatad da dukkan tarurrukan gwamnati, addini, wasanni, siyasa dss har na sawon makonni hudu.
A ranar Lahadi, kasar ta Ghana ta sanar da cewa za ta fara hana baki da kuma yan kasan da suka kwashe kwanaki 14 da suka gabata wajen kasar shiga kasar daga ranar Talata
Gwamnatin kasar ta dau wannan mataki ne bayan adadin wadanda suka kamu da cutar ya tashi daga biyu zuwa shida.

Asali: Twitter
KU KARANTA An kulle Masallacin Qudus saboda annobar Coronavirus
Mun kawo muku rahoton cewa Akalla kasashen nahiyar Afrika 26 cikin 54 da aka samu bullar annobar cutar Coronavirus kawo safiyar Litinin, 16 ga watan Maris, 2020.
Ga jerin kasashen nahiyar Afrikan da aka samu bullar yanzu
Algeria, Misra, Tunisiya, Maroko, Senegal, Najerya, Afrika ta kudu, Kamaru, Burkina Faso, Togo, DR Congo, Cote D'Ivoire, Habasha, Kenya, Namibia, Seychelles, Central African Republic, Congo, Equatorial Guinea, Eswatini, Gabon, Guinea, Mauritania, Ruwanda, Ghana da Sudan
A Najeriya, har yanzu mutane biyu aka tabbatar sun kamu da cutar, bayan haka, an gwada mutane 48 a jihohi irinsu Edo, Enugu, FCT, Kano, Lagos, Ogun, Rivers, da Yobe, kuma ba same su da it aba.
Ministan kiwon lafiya, Enahire, ya bayyana cewa dan kasar italiyan da ya kawo cutar Najeriya ya samu lafiya kuma nan ba da dadewa ba za a sallameshi.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng