Buhari da Gbajabiamila sun kebe a fadar shugaban kasa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga ganawa da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.
Duk da har yanzu dai ba a san abinda za su tattauna ba a taron, amma dai an san gwamnatin tarayya na kara duba shirin rage yawan kasafin kudin shekarar nan ta 2020 bayan faduwar farashin danyen man fetur sakamakon barkewar cutar Coronavirus a fadin duniya.
Kamar yadda ministar tsari da kasafin kudin kasa, Zainab Ahmed ta sanar, wannan yunkurin zai samu duba ne daga gwamnatin tarayya da kuma majalisar tarayyar kasar nan.
Karin bayani na nan tafe...
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng