Cutar Coronavirus ba ta shigo Yobe ba – Gwamnatin jahar

Cutar Coronavirus ba ta shigo Yobe ba – Gwamnatin jahar

- Gwamnatin Yobe ta ce cutar Coronavirus ba shigo jahar ba

- Ta ce an sallami mara lafiyan da ake zargin yana nuna alamu na cutar Coronavirus daga asibitin koyarwa na jami’ar jahar bayan gwaji ya nuna baya dauke da cutar

- Kwamishinan lafiya na jahar ya ce gwamnatin jahar ta tanadi cibiyoyin kebe wadanda ke dauke da cutar guda biyu koda za a samu a nan gaba

Gwamnatin jahar Yobe ta ce an sallami mara lafiyan da ake zargin yana nuna alamu na cutar Coronavirus daga asibitin koyarwa na jami’ar jahar bayan gwaji ya nuna baya dauke da cutar.

Da yake jawabi ga manema labarai a Damaturu, gwamishinan lafiya na jahar Yobe, Lawan Gana, ya ce babu bukatar tayar da hankali domin cutar Coronavirus bata shiga jahar ba.

Cutar Coronavirus ba ta shigo Yobe ba – Gwamnatin jahar

Cutar Coronavirus ba ta shigo Yobe ba – Gwamnatin jahar
Source: Twitter

Kwanaki shida da suka gabata, kamar yadda shirin daukar mataki ta tabadar, an kebe wani dan Najeriya da ke zama a California wanda ya kawo ziyara a asibitin koyarwa na jahar Yobe, inda aka ta kula dashi domin alamun cutar.

An dibi jinin mutumin zuwa Abuja domin duba kwayar cutar Coronavirus.

KU KARANTA KUMA: Za a hana masu laifi takarar Gwamna da Shugaban kasa a Najeriya

Sakamakon gwajin ya nuna baya dauke da cutar sannan gwamnatin jahar ta ce an salami mara lafiyan.

Kwamishinan lafiyan na jahar ya ci gaba da bayanin halin da ake ciki. Ya ce gwamnatin jahar ta tanadi cibiyoyin kebe wadanda ke dauke da cutar guda biyu koda za a samu a nan gaba.

Ya kara da cewa gwamnatin ta tanadi kayayayyaki domin hana yaduwar mummunan cutar ta Coronavirus.

A wani labari na daban mun ji cewa duk da kiraye kirayen da kungiyar ta’addanci ta duniya, ISIS, take yi ma mayakanta game da kai haddamar da hare hare a kasashen Turai, amma a yanzu ta ja da baya, inda ta nemi su kauce ma shiga nahiyar Turai saboda annobar cutar Corona.

Jaridar NewYork Times ISIS ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ta fitar a jaridarta na ‘Al-Naba’ indsa ta shawarci duk mayakanta dake turai, kuma har sun kamu da cutar, toh su yi zamansu a can domin cigaba da yada ta ga kafirai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel