Abubuwa 5 da duniya ta fuskanta cikin wannan shekarar ta 2020

Abubuwa 5 da duniya ta fuskanta cikin wannan shekarar ta 2020

Cikin kimanin kwanaki 75 da kwashe cikin sabuwar shekarar 2020, alummar duniya sun fuskanci akalla jarabawa biyar da basu taba gani ba ko ji a tarihi ba ko kuma an dade ba a yi ba

Akalla mutane 13000 sun mutu a fadin duniya, anyi asarar amfanin gona, yanayin rayuwar mutane ya sauya, tsoro da fargaba ta mamaye zukatan mutane.

Ga jerin abubuwan

01. Annobar Coronavirus

Shiga sabuwar shekara ke da wuya, wata sabuwar kwayar cuta ta bayyana a kasar Sin wacce ke kama mutane cikin kankanin lokaci.

Bayan watanni biyu da bullar cutar, mutane 276,000 suka kamu da ita, 13,000 sun mutu sakamakonta kuma 83,968 sun warke.

Cutar ta bulla a kasashe akalla 180 a duniya wanda ya hada da Amurka, Ingila, Jamus, Faransa, Saudiyya, Rasha, da sauransu.

02. Miliyoyin fari da dangwaye sun cika kasar Yamen da wasu kasashe a gabashin Afrika

Wasu fari sun bayyana a kasashen gabashin Afrika irinsu Habasha dss inda suke hallaka kayan gona.

An siffata farin a matsayin mafi hadari a tarihi kuma sun shiga kasashe irinsu Somaliya, Habasha, Sudan, Djibouti, Eriteriya, kuma akwai yiwuwan sun karasa kasar Uganda.

03. Rikicin addini a kasar Indiya

Rikicin addini ya barke a kasar Indiya tsakanin Mabiyar Hindu da Musulai inda aka kashe akalla mutaen 43, yawanci Musulmai, a gaban jamian tsaro tamkar da hannun gwamnati.

Rikicin ya samo asali ne bayan majalisar dokokin kasar ta samar da sabuwar dokar hana Musulmai shigo kasar Indiya da kuma zama yan kasa. Hakan bai yiwa Musulman kasar, har da wasu da ba Musulmai dadi ba.

04. Girgizan kasa a kasar Turkiyya

Mutane 41 sun hallaka yayinda 1,600 sun jikkata a gabashin kasar Turkiyya bayan girgizan kasa a ranar 24 ga Junairu, 2020.

Abin ya kai ga kasashen makwaftan Turkiyya irinsu Armeniya, Syiria da Iran sun girgiza.

05. Fashewar bututun gas a Legas Najeriya

An samu fashewar iskar gas ranar 15 ga Maris inda akalla mutane 17 suka rasa rayukansu kuma 15 suka jikkata a karamar hukumar Abule Ado ta jihar Legas.

Gidajen akalla 50 sun kone kuma anyi asarar miliyoyin dukiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel