Sarkin Kano: Shehu Sani ya bawa Sanusi II muhimmiyar shawara

Sarkin Kano: Shehu Sani ya bawa Sanusi II muhimmiyar shawara

- Sanata Shehu Sani ya aike wa tubabben sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II shawara

- Tsohon dan majalisar ya shawarci Sanusi kada ya bari wasu mutane ko kungiyoyi su tsunduma shi cikin siyasa

- Sani ya kuma shawarci Sanusi kada ya bari ayi amfani da shi domin cimma wata manufa

Tsohon dan majalisa, Sanata Shehu Sani ya bawa tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi II wasu shawarwari masu muhimmanci.

Idan ba a manta ba, gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya cire Sanusi daga kan karagar mulki a ranar Litinin 9 ga watan Maris kan rashin yi wa gwamnati biyayya.

Sanusi ya baro garin Awe na jihar Nasarawa inda aka tura shi bayan cire shi daga mulki ya koma birnin Legas ya hadu da iyalansa bayan kotu ta bayar da umurnin a kyalle shi ya tafi duk inda ya ke so.

Bayan sauke shi daga mulki, akwai hasashen cewa akwai yiwuwar Sanusi zai shiga siyasa ya yi takara.

DUBA WANNAN: Kwankwaso: Ina farin ciki domin wadanda suka yi garkuwa da Sanusi sun sake shi

Sai dai a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Asabar 14 ga watan Maris, Sanata Shehu Sani ya shawarci tsohon sarkin kada ya yarda a ja shi ya shiga siyasa.

Ya kuma shawarci sarkin da kada ya bari wasu kungiyoyi ko mutane su yi amfani da shi domin cimma matsayarsu.

Ya rubuta, "Ya kai Sanusi,

"Ka huta sosai tare da iyalanka yanzu da babu nauyin sarauta a kan ka; Ka guji mutanen da ke kokarin tsinduma ka a cikin siyasa kuma kada ka bari ayi amfani da kai. Zama jarumi kawai ya isa, su je su nemi shahidin su a wani muri."

A baya, Sanatan ya yi tsokaci a kan mukaman da gwamnan jihar Kaduna,Nasir El-Rufai ya bawa sarkin bayan an sauke shi.

Kasa da awanni 24 da sauke shi gwamnan ya nada Sanusi shugaban gudanarwa na KASU da kuma mamba na masu bayar da shawara na KADIPA.

A yayin da wasu ke yaba wa gwamnan saboda nuna goyon baya ga tsohon abokinsa, Sanata Shehu Sani bai yi wa abin irin wannan kalon ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel