Jerin kyautukan da wanda ya lashe gasar kamun kifi ta Argungun ya samu

Jerin kyautukan da wanda ya lashe gasar kamun kifi ta Argungun ya samu

Abubakar Ya’u daga karamar hukumar Augie ta jihar Kebbi ne ya bayyana zakaran gwajin dafi wajen gasar kamun kifin da aka yi a Argungun. Ya samu kyautar naira miliyan goma, sabbin motoci biyu da kuma kujerun Makka biyu sakamakon nasarar kamo kifin da yafi kowanne girma mai nauyin 78kg.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, Ya’u ya zama mai nasara a cikin masunta sama da 50,000 da suka taka rawar gani wajen gasar kamun kifin a jihar Kebbi a wannan shekarar.

Bala Yahaya Bagaye ne yazo a na biyu inda yayi nasarar kama kifi mai nauyin 75kg, yayin da Sani Maiwake ya zo a na uku da kifinsa mai nauyin 70kg.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, Simon lalong ya ba wa wanda yazo a na farko kyautar naira miliyan 3, na biyun naira miliyan biyu sai na uku naira miliyan daya.

Hassan Bello, babban sakataren kungiyar masu jiragen ruwa ta Najeriya, ya gabatar da kyautar naira miliyan daya ga wanda yayi nasarar zuwa na farko, na biyu kuwa ya samu N750,000 sai na uku ya samu N500,000.

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya bada kyautar naira miliyan uku ga na farko, na biyu ya samu naira miliyan biyu inda na uku ya samu naira miliyan daya da kuma kujerun hajji.

Jerin kyautukan da wanda ya lashe gasar kamun kifi ta Argungun ya samu
Jerin kyautukan da wanda ya lashe gasar kamun kifi ta Argungun ya samu
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Har yanzu Sanusi ne shugaban gudanarwa na jami'ar Ekiti - Shugaban Jami'a

Kamfanin auduga na yammacin Afirka, WACOT ya bada mota sabuwa da kuma naira miliyan daya da kujerar hajji ga na farkon. Hajiya Zainab bagudu, uwargidan gwamnan jihar Kebbi, ta bada kyautar mota dalleliya ga wanda yazo a na farkon.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, kamfanin Maltina ta bada kyautar Keke Napep ga na daya sai Babura ga na biyu da na uku.

A yayin jawabi a taron, bako na musamman kuma shugaban majalisar dattijan Najeriya, Ahmed Lawal, ya ce wannan bikin na nuna al’adun Najeriya ne karara.

“Idan na kalla wajen kamun kifin nan, sai in ce ‘Ya Ubangiji, ka albarkacemu’; abinda muke bukata shine amfani da albarkatun nan yadda ya dace. An fara wannan gasar ne tun a 1934 kuma an dakatar da shi ne tun shekaru 10 da suka gabata saboda rashin tsaro.” cewar Lawan

“Dole ne mu gode wa Ubangiji da ya bamu damar yin wannan gasar tare da jinjinawa sojinmu da suka samar mana da tsaro a kasar nan,” yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel