Baje kolin gasar kamun kifi ta Argungu a jihar Kebbi (Hotuna)
A ranar Alhamis ne aka bude bikin baje kolin kamun kifi na Argungun da kuma al'adun gargajiya na jihar Kebbi.
Wannan ne karo na farko a cikin shekaru 11 da ake gasar baje kolin kamun kifin tun bayan da aka dakatar da ita saboda rashin tsaro a kasar nan.
Wannan dai bikin ya samu halartar manyan mutane daban-daban a fadin kasar nan. A ranar da aka kaddamar da bikin, Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ne ya je har jihar inda ya bude bikin.
DUBA WANNAN: Har yanzu Sanusi ne shugaban gudanarwa na jami'ar Ekiti - Shugaban Jami'a
Mai magana da yawun shugaban kasa Buhari, Mista Femi Adesina ne ya bayyana haka inda yace shugaba Buhari ya bayyana dawowar bikin a matsayin wata manuniya dake nuni ga nasarar da gwamnatinsa ta samu wajen inganta tsaro a Najeriya.
Buhari ya maimaita manufar gwamnatinsa na cigaba da inganta harkar tsaro domin habbaka bukukuwan al’adu da yawon bude ido, tare da janyo masu zuba hannu jari a bangaren nishadantarwa na Najeriya.
Haka zalika Buhari ya bayyana cewa akwai ire iren bukukuwan al’adu na Argungu da ake gudanarwa a duk fadin kasar nan, wanda ke kara dankon zumunci a tsakanin yan Najeriya tare da nuna ire iren al’adun dake kasar nan ga bakin kasashen waje.
Shugaban kasa ya bayyana cewa a shekarar 2015 gwamnatinsa ta kaddamar da tsarin samar da abincin don ciyar da al’ummar kasa a jahar Kebbi, kuma duba da amfanin gona da aka bajekolinsu a taron ya nuna an samu nasara gagaruma ga tsarin siyar da kasa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng