Bayan korata a wajen aiki iyalina ta gudu, yanzu kuma tana so ta dawo bayan taji na sami miliyan 15 - Wani na neman shawara

Bayan korata a wajen aiki iyalina ta gudu, yanzu kuma tana so ta dawo bayan taji na sami miliyan 15 - Wani na neman shawara

Wani mutumi mai suna Jimoh Kazeem yana neman shawara a wajen al'umma akan wata matsala da take damunsa matuka

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa matarsa da suka yi aure shekarar da ta gabata, watanni biyu da suka wuce ta gudu ta barshi, inda ta ce baza ta iya zama da mutum marar aikin yi ba, bayan haka kuma ta kwashe komai na gidan, inda ta kai ga ya koma rokar wasu abubuwan a wajen makota da abokanan sa.

Sai dai kuma cikin ikon Allah, bayan watanni shida da faruwar wannan lamari wajen da yake aikin suka kira shi suna bashi hakuri akan cewa kuskurene ya sanya suka kore shi ba, inda har suka bashi kyautar naira miliyan sha biyar a matsayin toshiyar baki.

Matarsa na jin wannan abu da ya faru dashi, sai ta fara neman shi tana bashi hakuri akan ya yafe mata tana so ta dawo.

Ga dai rubutun da yayi a shafin nasa na Facebook cikin harshen Turanci:

KU KARANTA: An tabbatar da samun cutar Coronavirus a jikin shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro

"Shekaruna 26, amaryata kuma shekarunta 28, mun yi aure shekarar da ta gabata, amma bayan auren mu sai na rasa aikina hakan ya saka matata ta gudu ta barni, bayan mako daya ta dawo ta kwashe komai na gidan, na cigaba da rayuwa haka ni daya, ina bacci a kasa na tsawon watanni shida.

"Kawai watarana sai na samun kiran waya daga wajen dana yi aiki, aka bayyana mini cewa kuskurene ya sanya aka kore ni da laifin cewa na saci kudi, yanzu an kama barawon, saboda haka za a mayar dani bakin aiki, sannan kamfanin zai biyani duka albashin dana rasa a baya da kuma alawus.

"Lokacin dana koma wajen aiki an bani kudi naira miliyan goma sha biyar (N15,000,000) a matsayin albashi da alawus dina. Yanzu matsalar shine matata na son ta dawo bayan taji cewa na samu wannan kudi kuma na koma aiki.

"Shin wace shawara zaku bani, na saketa ne ko kuma na dawo da ita?

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel