Daga karshe: Sanusi II ya bayyana wadanda suka bada umarnin tsare shi

Daga karshe: Sanusi II ya bayyana wadanda suka bada umarnin tsare shi

- Lamido Sanusi ya ce an tube masa rawani ne ba tare da an bi ka’ida ba kuma hakan ba zai sa ya dauka mataki ba

- Gwamnatin jihar Kano ta tube rawanin Sarkin Kano na 14 ne bayan majalisar zartarwar jihar ta amince

- Ya yi ikirarin cewa Antoni janar na jihar Kano, Ibrahim Mukhtar da kuma Antoni janar na tarayya, Abubakar Malami ne suka bada umarnin tsaresa

Lamido Sanusi II ya ce an tube masa rawani ne ba tare da an bi ka’ida ba kuma hakan ba zai sa ya dauka mataki a kan gwamnatin jihar Kano ba, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Tsohon gwamnan bankin, wanda ya samu matsala da gwamna Umar Ganduje na jihar Kano tun 2017, an koresa daga jihar ne a ranar Litinin a sakamakon zarginsa da aka yi da rashin biyayya ga gwamnatin jihar.

Gwamnatin jihar Kano ta tube rawanin Sarkin Kano na 14 ne bayan majalisar zartarwar jihar ta amince. Ta kara da cewa Sanusi baya halartar tarukan da gwamnatin ta shirya ba tare da wani dalili ba wannan ta ce wannan adawa ce.

Daga karshe: Sanusi II ya bayyana wadanda suka bada umarnin tsaresa
Daga karshe: Sanusi II ya bayyana wadanda suka bada umarnin tsaresa
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Sanusi yana da 'yancin zuwa ko wane gari, har da Kano - El-Rufai

Sanusi wanda yace an gagara bashi damar sauraro wanda hakan yasa aka tube masa rawani, ya ce umarnin kama shi, mayar da shi jihar Nasarawa daga Kano da kuma tsaresa da aka yi garin Awe na jihar Nasarawa, ya zo ne daga Abuja.

Ya yi ikirarin cewa Antoni janar na jihar Kano, Ibrahim Mukhtar da kuma Antoni janar na tarayya, Abubakar Malami ne suka ba hukumar jami’an tsaro na farin kaya da ‘yan sanda tsare shi.

Sanusi ya ce an hantaresa tare da gaggauta fitar dashi daga fadar ba tare da ya dauka kayan da suke mallakinsa ba. Ya ce bayan sauke rawaninsa, wani abokinsa ya turo jirgin da zai kai shi Legas daga jihar Kano amma sai kwamishinan ‘yan sandar jihar yace a kai shi Abuja.

Sanusi ya sanar da wannan ne a karar da ya shigar a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel