Kasar Amurka ce ta kawo mana cutar Coronavirus don ta bata sunan mu a idon duniya - Zargin kasar China

Kasar Amurka ce ta kawo mana cutar Coronavirus don ta bata sunan mu a idon duniya - Zargin kasar China

- Wani rubutu da wani babba kuma masani a fannin lafiya na kasar China ya wallafa a shafinsa na Twitter

- Ya nuna yadda ya zargi kasar Amurka da hannu a bullar cutar Coronavirus a kasar ta China

- Ya bayyana cewa sojojin Amurka ne suka shiga da cutar kasar ta China

Wani babba a kasar China ya bayyana cewa sojojin kasar Amurka ne suka kai musu cutar nan mai kisa ta Corona kasar ta China, duk kuwa da bai bayar da wata kwakkwarar shaida ba.

Mai magana da yawun ma'aikatar kasashen waje na kasar Zhao Lijian, shine ya bayyana haka a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis dinnan da ta gabata.

Idan ba a manta ba a baya shugaban cibiyar kula da manyan cutuka da bakin shi ya bayyana cewa cutar ta samo asali ne ta hanyar sayar da namun daji da ake yi a kasuwannin birnin na Wuhan.

Amma a 'yan kwanakin nan, wani babba a kasar ta China din kuma masani a fannin lafiya ya zargi cewa cutar ta samo asali ne daga wani waje daban, bayan Beijing ta caccaki kasar Amurka da kiran cutar da suna 'Cutar Wuhan'.

A cikin rubutun da ya wallafa, Zhao ya sanya bidiyo na cibiyar lura da manyan cutuka ta kasar Amurka, inda ya tabbatar da cewa wasu 'yan Amurka da suka mutu sanadiyyar mura, an tabbatar da samun cutar a jikinsu.

KU KARANTA: Sha'awa na damunmu, muna bukatar maza don kwanciya - Matan gidan yari

"Akwai yiwuwar Amurka ce ta kawo mana cutar birnin Wuhan. Muna bukatar bayani daga wajen kasar Amurka."

Sakataren kasar Amurka ya fusata kasar ta China, bayan ya danganta cutar da kasar ta China, inda ya kira ta da cutar 'Cutar Wuhan'.

A yanzu dai sama da mutane 130,000 ne suka kamu da cutar, sannan kusan mutum 5,000 ne suka mutu a fadin duniya sanadiyyar cutar.

Robert O'Brien, mai bada shawara ta musamman a fannin tsaro na kasar Amurka, ya bayyana cewa cutar ta samo asali ne daga kasar China.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel