Ayarin motocin mataimakin shugaba Osinbajo sun gamu da mummunan hatsari a Abuja

Ayarin motocin mataimakin shugaba Osinbajo sun gamu da mummunan hatsari a Abuja

Ayarin motocin mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo sun gamu da mummunan hadari a babban birnin tarayya Abuja yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa filin sauka da tashin jirage na Nnamdi Azikwe.

Jaridar TheCable ta ruwaito hadarin ya faru ne a ranar Juma’a, 13 ga watan Maris yayin da Osinbajo yake kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin domin wata tafiya da zai yi zuwa jahar Legas.

KU KARANTA: Babu wanda buge ni, balle harbi – Inji Jameel Bello, matashin da ya janyo hatsaniya a Kebbi

Majiyar Legit.ng ta ruwaito guda daga cikin Yansandan dake cikin tawagar Osinbajo, wanda ke tuka babur yana gyara ma ayarin motocin hanya, ya rasu a sakamakon mummunan hadarin.

Hadimin mataimakin shugaban kasa ta bangaren watsa labaru, Laolu Akande ya tabbatar da mutuwar, inda yace: “Tare da jimami da alhini, muna sanar da mutuwar guda daga cikin Yansandan dake ayarin motocin shugaban kasa, Sufeta Ali Gomina mai shekaru 45, wanda hatsarin ya rutsa da shi a yau.

“Hatsarin ya faru ne a kan hanyar zuwa filin jirgi na Nnamdi Azikwe, mataimakin shugaban kasa ya ji zafin mutuwar, wanda hakan yasa ya fasa tafiyar da zai yi.

“Mataimakin shugaban kasan ya bayyana Gomina a matsayin mutumin kirki, mai jajircewa a kan aikinsa, wanda ya mutu ya bar babban gibi, ya mutu ya bar yara da yan uwa.”

A wani labarin kuma, matashin nan da ya janyo hatsaniya a garin Argungu na jahar Kebbi, Mohammed Jameel Bello ya musanta rahotannin da ake yadawa na cewa wai jami’an hukumar DSS sun bude masa wuta bayan yayi kokarin damkan shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Idan za’a tuna shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci bikin al’adun gargajiya na kamun kifi da noma da aka gudanar a garin Argungu na jahar Kebbi karo na farko bayan kwashe tsawon shekaru 11 ba tare da an yi shi ba.

Sai dai ba kamar yadda aka yi ta yayatawa ba, Bello yace babu wanda ya harbe shi, kuma ya samu kulawa kyakkyawa daga wajen jami’an tsaro, wadanda yace har abinci suka ba shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel