Sanusi II zai shugabanci lakca din yayen dalibai a LASU

Sanusi II zai shugabanci lakca din yayen dalibai a LASU

Tsohon sarkin Kano, Malam Sanusi Lamido zai shugabanci lakcar yayen dalibai karo na 24 na jami’ar jihar Legas, cewar shugaban jami’ar jihar Legas, Farfesa Olanrewaju, SAN.

Fagbohun, wanda ya zanta da manema labarai a kan shirin bikin yayen daliban a ranar Juma’a, ya jaddada cewa an kammala tsarin cewa Sanusi ne zai jagoranci bikin yayen daliban tun kafin abinda ya auku a jihar Kano ya faru.

Shugaban jami’ar ya kara da cewa akwai mutanen da suka taka rawar gani wajen kawo ci gaba a makarantar duk ana shirin karrama su.

Sun hada da tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, Babatunde Fashola da kuma tsohon shugaban makarantar. Ya bayyana cewa za a ba mutanen digirin girmamawa ne.

Daga cikin wadanda za a karrama din akwai Sanata Remi Tinubu, Gimbiya Adejoke Orelope-Adefulire, Aderemi Makanjuola, Mai shari’a Opeyemi Oke, Dr. Oba Otudeke da Segun Agbaje.

Sanusi II zai shugabanci lakca din yayen dalibai a LASU

Sanusi II zai shugabanci lakca din yayen dalibai a LASU
Source: UGC

DUBA WANNAN: Mahaifiyar tubabben Sarki Sanusi II ta kai masa ziyara a Nasarawa (Bidiyo)

Fagbohun ya bayyana cewa dalibai 76 ne suka samu shaidar digiri mai darajar farko daga cikin 6,197 da za a yaye.

“Sauran wadanda za a yaye din akwai masu digiri matsayi na biyu 1,183, sai masu digiri matsayi na uku sun kai 4,494. Masu digiri matsayi na hudu sun kai 418 sai kuma digiri mai matsayi na biyar mutane 26." yace.

Ya kara da cewa, "Ina farin cikin sanar daku cewa dalibi mafi kwazo a zango na 2018/19 shine Shotunde Oladimeji Idris daga sashen karatun kasuwanci. Ya samu jimillar 4.95,”

Fagbohun ya kara da cewa wannan ne karo na farko da sashen karatun harshen turanci ya samar da dalibi mai digiri mai daraja ta farko.

A yayin jero wasu daga cikin nasarorin da makarantar ta samu a shekara daya da ta gabat, shugaban makarantar yace malaman makarantar sun samu lambar yabo a fannin bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel