Babu wanda buge ni, balle harbi – Inji Jameel Bello, matashin da ya janyo hatsaniya a Kebbi

Babu wanda buge ni, balle harbi – Inji Jameel Bello, matashin da ya janyo hatsaniya a Kebbi

Matashin nan da ya janyo hatsaniya a garin Argungu na jahar Kebbi, Mohammed Jameel Bello ya musanta rahotannin da ake yadawa na cewa wai jami’an hukumar DSS sun bude masa wuta bayan yayi kokarin damkan shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Idan za’a tuna shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci bikin al’adun gargajiya na kamun kifi da noma da aka gudanar a garin Argungu na jahar Kebbi karo na farko bayan kwashe tsawon shekaru 11 ba tare da an yi shi ba.

KU KARANTA: Hukumar kula da shige da fice ta kammala shirin daukan matasan Najeriya aiki

Mai magana da yawun shugaban kasa Buhari, Mista Femi Adesina ne ya bayyana haka inda yace shugaba Buhari ya bayyana dawowar bikin a matsayin wata manuniya dake nuni ga nasarar da gwamnatinsa ta samu wajen inganta tsaro a Najeriya.

Daily Trust ta ruwaito an hangi matashin yana ta kokarin kusantar shugaba Buhari a daidai lokacin da ya tsaya tare da manyan baki domin daukan hoto, kwatsam sai ya kutsa kai har gab da Buhari, da kyar jami’an tsaro suka cimimiye shi.

Sai dai ba kamar yadda aka yi ta yayatawa ba, Bello yace babu wanda ya harbe shi, kuma ya samu kulawa kyakkyawa daga wajen jami’an tsaro, wadanda yace har abinci suka ba shi.

Bugu da kari, Bello yace abin da ya yi, ya yi ne duk a cikin shaukin kaunar shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma yace haduwarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari shi ne babban burinsa a rayuwa, ya kara da cewa koda a ce ma an harbe shi, shi kam bukatarsa ta biya.

Babu wanda buge ni, balle harbi – Inji Jameel Bello, matashin da ya janyo hatsaniya a Kebbi

Babu wanda buge ni, balle harbi – Inji Jameel Bello, matashin da ya janyo hatsaniya a Kebbi
Source: Facebook

A jawabinsa, kaakakin shugaban kasa Malam Garba Shehu game da lamarin, sai yace: “Masoyin shugaban kasa ne mai rawar kai wanda yayi kokarin kusantar shugaban, amma bai san ya wuce gona da iri ba.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel