Mahaifiyar tubabben Sarki Sanusi II ta kai masa ziyara a Nasarawa (Bidiyo)

Mahaifiyar tubabben Sarki Sanusi II ta kai masa ziyara a Nasarawa (Bidiyo)

A yau ne mahaifiyar tubabben sarki Sanusi II ta ziyarcesa a garin Awe da ke jihar Nasarawa inda ya samu mafaka bayan tube masa rawani da gwamna Abdullahi Ganduje yayi a jihar Kano.

Kamar yadda wani bidiyo da gidan talabijin na Channels ya fitar, an kara tsaro a inda aka sauke sarkin a garin Awe da ke jihar Nasarawa.

Jami'an tsaro da na NSCDC duk sun hallara tare da kara tsaro a gidan da mai martaban yake.

Daga nan kuwa sai ga mahaifiyar tsohon sarkin na fitowa daga motar da ta iso tare da shiga cikin gidan.

Idan zamu tuna, yau ne rana ta farko da tsohon sarkin ya fara fitowa cikin jama'a tun bayan da aka tube masa rawani tare da kai shi jihar Nasarawa.

DUBA WANNAN: Sarkin Loko ya bayyana abinda suka tattauna da Sanusi II a daren da ya kwana a garinsa

bangare guda, Babban kotun tarayya da ke Abuja a ranar Juma'a ta bayar da umurnin sakin tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II daga inda aka tsare shi a garin Awe na jihar Nasarawa bayan an cire daga kan mulki a ranar Litinin.

Mai shari'ar Anwuli Chikere ne ta bayar da umurnin sakamakon bukatar da shugaban lauyoyinsa, Latee Fagbemi (SAN) ya shigar a ranar Juma'a. Kotun ta ce a mika takardan umurnin sakin Sanusi da dukkan hukumomin da suka tsare da shi.

Wadanda Sanusi ya yi karar su a kotun kan batun tsare shi suna hada da Sifeta Janar na 'yan sanda, Muhammad Adamu; Shugaban hukumar DSS, Yusuf Bichi; Attony Janar na jihar Kano, Ibrahim Mukhtar da Ministan Shari'a na Najeriya, Mista Abubakar Malami (SAN).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel